Ina nan da raina ban mutu ba – Tsohon kwamishinan yan sandan Kano, CP Muhammad Wakili

Ina nan da raina ban mutu ba – Tsohon kwamishinan yan sandan Kano, CP Muhammad Wakili

- CP Muhammed Wakil, tsohon kwamshinan yan sandan jihar Kano ya karyata rade-radin mutuwarsa

- Tsohon kwamishinan wanda aka fi sani da Singam ya ce yana nan cike da koshin lafiya da kwanciyar hankali

- A jiya Talata ne aka yi ta yada jita-jitan cewa ya rasu a hatsarin mota a shafukan sadarwa

Tsohon kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Muhammad Wakili wanda aka fi sani da Singam ya yi watsa da rahotannin cewa Allah ya amshi ransa a wani hatsarin mota.

An tattaro cewa wasu labarai sun yadu shafukan zumunta a daren ranar Talata game da zargin mutuwarsa a hatsarin mota, inda mutane suka ta wallafa hotunansa tare da yi masa fatan samun rahamar Allah.

A wata hira da yayi da sashin Hausa na BBC, CP Singam mai ritaya ya bayyana cewa yana nan da ransa kuma cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali.

Ina nan da raina ban mutu ba – Tsohon kwamishinan yan sandan Kano, CP Muhammad Wakili
Ina nan da raina ban mutu ba – Tsohon kwamishinan yan sandan Kano, CP Muhammad Wakili Hoto: BBC
Source: UGC

KU KARANTA KUMA: Karya dokar korona: An tsare akalla mutane 200 a Kano, 25 sun tafi gidan gyara hali

Ya ce:

"Ban san ta inda wannan labarin ya billoba, ban san hujjarsu kan haka ba, ban san me suke son su cimma da wannan abu ba, wannan al'amari ya sa mutane damuwa, tun 11 na dare ake ta kira na domin a tabbatar da gaskiyar wannan labari.”

Ya ci gaba da cewa ya samu labarin ne sakamakon kiransa da wani babban mutum ya yi, bayan ya ci karo da labaran a shafukan sada zumunta, abin da ya sa hankalinsa ya tashi ya kira wayarsa domin ya tabbatar ko gaskiya ne.

CP Wakili ya kara da cewa:

''Ina da lambarsa, na fada a raina, lafiya kuwa da daren nan na ga kiransa?, ina dagawa na ce yallaɓai lafiya?, sai kawai na ji yana ta cewa Alhamdulillahi... Alhamdulillahi.. ai ga abin da ke faruwa ana ta cewa ka rasu.”

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa Shugaba Buhari ba zai taba barin Fani-Kayode ya koma APC ba, jigon jam’iyya

Ya kuma yi kira ga masoyansa, su kwantar da hankalinsu, yana cewa yana nan cikin ƙoshin lafiya.

A wani labarin, tsohon mai tsaron baya na kungiyar kwallon Nigeria, Super Eagles, Yisa Sofoluwa ya rasu a ranar talata da yamma a sashin masu bukatar kulawa ta musamman na asibitin koyarwa ta jami'ar Legas.

The Punch, a ranar Juma'a ta ruwaito cewa Sofoluwe yana fama da rashin lafiya bayan gwaji ya nuna yana fama da ciwon 'mild cerebral atrophy' mai alaka da kwakwalwa.

Wani daga cikin abokansa na kusa, Waidi Akanni da tsohon mai tsaron gidan Super Eagles, Dosu Joseph sun tabbatar da rasuwarsa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel