Rikicin makiyaya: Buhari ba mai yawan magana bane, ba zai iya magana a kan komai ba, fadar shugaban kasa

Rikicin makiyaya: Buhari ba mai yawan magana bane, ba zai iya magana a kan komai ba, fadar shugaban kasa

- Shugaba Buhari ba zai iya yin magana a kan kowane batu ba, fadar shugaban kasa ta bayyana

- Da yake magana kan lamuran makiyaya a kasar, Femi Adesina ya ce za a saurari ra'ayoyi daban-daban sannan za a yi amfani da wanda ya fi rinjaye

- A halin yanzu, Ganduje ya yi kira ga hana zirga-zirgar shanun daga arewa zuwa kudu

Shugaba Muhammadu Buhari ba zai iya mayar da martani ga kowane ra'ayi ko magana ba a cewar fadar shugaban kasa.

Femi Adesina, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan kafofin watsa labarai ne ya bayyana hakan a ranar Talata, 9 ga watan Fabrairu, jaridar The Punch ta ruwaito.

Adesina na mayar da martani ne ga kiran da fitattun ‘yan Najeriya kamar Wole Soyinka ke yi ma shugaban kasa Muhammadu Buhari na magance matsalar makiyaya.

Rikicin makiyaya: Buhari ba mai yawan magana bane, ba zai iya magana a kan komai ba, fadar shugaban kasa
Rikicin makiyaya: Buhari ba mai yawan magana bane, ba zai iya magana a kan komai ba, fadar shugaban kasa Hoto: @MBuhari
Source: Twitter

KU KARANTA KUMA: Ina nan da raina ban mutu ba – Tsohon kwamishinan yan sandan Kano, CP Muhammad Wakili

Hasali ma, gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, a nasa bangaren ya yi kira da a samar da dokar da za ta hana zirga-zirgar da makiyaya ke yi da shanu daga arewacin kasar zuwa wasu sassan.

Kuma da yake martani, Adesina ya ce:

“Idan kuna da matsala irin wannan, za a sami ra'ayoyi da yawa, za a nemi hanyoyin magance su da yawa. Ba lallai ba ne sai shugaban ya yi magana a kan kowannensu.

“Ba dole ne sai ya yi hakan ba, kawai dai ra'ayin mutane za a ji. Sai ayi duba cikin lamarin sannan idan na bai daya ne, sai a karba. Amma ba wai da ra'ayi daya ya zo sai shugaban kasa yayi magana a kai, sannan wata dabara ta kuma zuwa, sai shugaban kasar yayi magana a kanta, irin wannan dole sai dai daga shugaban kasa mai yawan magana."

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa Shugaba Buhari ba zai taba barin Fani-Kayode ya koma APC ba, jigon jam’iyya

A wani labarin, gwamnoni a Arewa a ranar Talata sun bayyana batun kiwo a fili da makiyaya suke yi a matsayin tsohon abu. Ya kamata ya kare, The Nation ta ruwaito.

Wannan shawarar ita ce sakamakon, taron kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya, wanda aka gudanar.

Shawarar ta yi daidai da ra'ayin gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, wanda ya ce ya kamata makiyaya su rungumi kiwo a waje daya su daina kiwon shanun su daga Arewa zuwa Kudu shi ne zaman lafiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel