Femi Fani-Kayode ya bayyana dalilin da yasa ya gana da shugabannin APC

Femi Fani-Kayode ya bayyana dalilin da yasa ya gana da shugabannin APC

- Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya bayyana abinda yasa ya ziyarci shugabannin APC

- Fani Kayode ya ce sun gana ne domin tattauna kan batutuwan da suka shafi kasa da siyasa da nufin kare kasar daga tsinduma cikin yaki

- Ya kara da cewa a matsayinsu na dattawan kasa idan matsala ta taso dole ne a ajiye siyasa a gefe a hada kai domin cigaban kasa

Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani Kayode ya ce ya gana da shugabannin jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ne domin tattaunawa kan "halin da kasa ke ciki da harkokin siyasa da matakan da za a dauka don cigaba."

Fani-Kayode, a jiya ya gana da Shugaban riko na jam'iyyar APC na kasa, Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe da Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi.

Femi Fani-Kayode ya bayyana dalilin da yasa ya gana da shugabannin APC
Femi Fani-Kayode ya bayyana dalilin da yasa ya gana da shugabannin APC. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Hotunan hatsabibin mai garkuwa da aka kama yayin da ya tafi karbar kuɗin fansa

Hotunan taron na su ya sanya wasu sun fara hasashen cewa Fani-Kayode wanda dan jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ne na shirin sauya sheka ne zuwa APC duk da cewa yana cikin manyan masu sukar jam'iyyar.

A sanarwar da ya fitar ta shafinsa na Twitter a ranar Talata, Fani-Kayode ya ce taron da suka yi na sada zumunci ne da hada hannu domin ceto Nigeria daga tsindumawa cikin yakin basasa.

Ya ce baya ga shugabannin na jam'iyyar APC, yana ganawa da shugabannin wasu jam'iyyun siyasar.

"A jiya, na gana da shugaban jam'iyyar APC na kasa, Gwamna Mai Buni na Yobe da Gwamna Yahaya Bello na Kogi. Mun tattauna halin da kasa ke ciki, siyasar jam'iyyu da yadda za a ciyar da kasa gaba," a cewar wani sashi na sanarwarsa.

KU KARANTA: Buhari ya naɗa ni shugaban soji ne saboda ƙaunar da mahaifina ke masa, in ji Buratai

A cewar Fani Kayode, babban sharrin da kasar ke fuskanta shine yiwuwar fadawa yakin basasa na biyu don haka ya zama dole a ajiye banbancin siyasa don ganin cewa kasar ba ta fada mummunan hali ba.

Daga karshe ya yi addu'ar Allah ya taimaki Nigeria ya kuma yi mana jagora baki daya.

A wani labarain daban, babban malamin Kano, Shaikh Abduljabbar Nasir Kabara ya ce rufe masallacinsa da hana shi yin wa'azo da gwamnatin jihar ta yi "zalunci ne", kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Malamin ya ce gwamnatin da kanta, ta bakin kwamishinan ilimi na jihar, ta tabbatar da cewa abinda ake yi masa zalunci ne amma ta dakatar da shi ba tare da bashi damar ya kare kansa ba.

Abdul-jabbar ya yi wannan jawabin ne biyo bayan rufe masallacinsa da ke makarantarsa da gwamnatin Kano ta yi a ranar Laraba gami da hana saka karuntunsa a gidajen rediyo da kafafen sada zumunta na jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel