Bayan watanni 5, Jama’a su na cigiya a Twitter, ‘Ina Aisha Buhari ta shiga?’

Bayan watanni 5, Jama’a su na cigiya a Twitter, ‘Ina Aisha Buhari ta shiga?’

- An yi tsawon wata da watanni ba a ga Aisha Muhammadu Buhari a fili ba

- Rabon da mutane su ga uwargidar shugaban Najeriya tun cikin Satumba

- Rade-radi na yawo cewa mai dakin shugaba Buhari ta tare a birnin Dubai

People Gazatte ta ce uwargidar shugaban Najeriya, Aisha Muhammadu Buhari ta dauki tsawon lokaci ba ta bayyana a fili ba, tun bayan bikin ‘diyarta a bara.

Bayan an daura auren Hannan Buhari a Satumban 2020 ne aka daina jin duriyar matar shugaban kasa. Ana ta rade-radi cewa ta koma birnin Dubai, UAE, da zama.

Ko kafin wannan lokaci, uwargidar shugaban Najeriyar ta shafe kwanaki ba ta nan. A wancan lokaci an ce Aisha Buhari ta je duba likitan wuya ne a kasar UAE.

Bayan bacewar da mai dakin shugaba Muhammadu Buhari, ta kuma daina magana a shafinta na Twitter.

KU KARANTA: Abin da ya kai Aisha Buhari Dubai - Inji Hadiminta

Rabon Aisha Buhari da magana a Twitter tun a farkon Nuwamba, kusan watanni uku kenan. A watan Oktoba ta fito ta na kira a inganta sha'anin tsaro a Arewa.

Jaridar People Gazette ta ce rabon uwargidar shugaban Najeriyar da mahaifar maigidanta, Daura kuwa tun a watan Maris, 2019, lokacin da aka gudanar da zabe.

Da aka tuntubi hadiman matar shugaban; Suleiman Haruna da Aliyu Abubakar, sun ki cewa komai.

Mutane a Twitter sun tashi a yau su na maganar matar shugaban kasar. Oktopsy ya ce: "@seunokin, idan za ka yi hira da wani magoyin Buhari, ka tambaye sa ina Aisha Buhari ta shiga?"

KU KARANTA: Aisha Buhari ta dawo daga Dubai

Bayan watanni 5, Jama’a su na cigiya a Twitter, ‘Ina Aisha Buhari ta shiga?’
Hajiya Aisha Buhari Hoto: www.thenigerianvoice.com
Asali: UGC

Okolie Chinazom ta ce: "Mutanen wannan zamani su na da saurin mantuwa. Mutane sun daina tambayar ina Aisha Buhari ta ke?"

Wata mai suna Duchess of Lekki a Twitter, ta ce ba ta taba ganin mai dakin shugaban da ta bar gida a lokacin da mai gidanta yake mulki ba sai Aisha Buhari.

"Ina Aisha Buhari? Shin ko ba ita ba ce uwargidar shugaban Najeriya ne? Mu na bukatar amsar wannan", a cewar Hasan Husein

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel