Uwargidar shugaba kasa, Aisha Buhari, ta dawo daga Dubai

Uwargidar shugaba kasa, Aisha Buhari, ta dawo daga Dubai

Uwargidar shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari, ta dawo gida daga Dubai, hadaddiyar masarautar Larabawa UAE, Daily Trust ta ruwaito majiya nai karfi a fadar shugaban kasa.

Rahoton ya kara da cewa babu gaskiya cikin magana cewa tare da Hanan, diyar Buhari dake shirin daurin aure ranar 4 ga Satumba, 2020, aka tafi Dubai.

Hakazalika majiyar ta bayyana cewa babu gaskiya cikin rahoton cewa saura kiris jirgin da Hajiya Aisha ke ciki yayi hadari, amma an dan samu tangarda a cikin hazo.

Mun kawo muku rahoton cewa uwargidan buhari ta tafi Dubai duba lafiyan jikinta ne.

Uwargidar shugaba kasa, Aisha Buhari, ta dawo daga Dubai
Uwargidar shugaba kasa, Aisha Buhari, ta dawo daga Dubai
Asali: UGC

A ranar 7 ga Agusta, mun kawo muku rahoton cewa an garzaya da uwargidan shugaba Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha Buhari, birnin Dubai, kasar UAE don jinyan ciwon wuyan da take fama da shi tun bayan zuwanta Legas, Daily Trust ta ruwaito.

An samu labarin cewa uwargidan shugaba Muhammadu Buhari ta tafi Dubai ne tun washe garin Sallah sakamakon ciwon wuya da take fama dashi bayan komawa birnin tarayya Abuja daga jihar Legas.

Yayinda ta koma Abuja, ta killace kanta na tsawon makonni biyu saboda ciwon wuyan da take fama da shi na kimanin wata daya bayan ta'aziyyar.

Abin ya tayar da hankalin na kusa da uwargidar kuma hakan ya sa aka garzaya da ita birnin Dubai don ganin Likita.

KU KARANTA: Bayan Jigawa, Bauchi, Yobe, Musulman Lauyoyin Kaduna sun yi hannun riga taron gangami saboda janye gayyatar El-Rufa'i

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel