Yanzu-yanzu: An garzaya da Aisha Buhari Dubai jinyan rashin lafiya

Yanzu-yanzu: An garzaya da Aisha Buhari Dubai jinyan rashin lafiya

An garzaya da uwargidan shugaba Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha Buhari, birnin Dubai, kasar UAE don jinyan ciwon wuyan da take fama da shi tun bayan zuwanta Legas, Daily Trust ta ruwaito.

An samu labarin cewa uwargidan shugaba Muhammadu Buhari ta tafi Dubai ne tun washe garin Sallah sakamakon ciwon wuya da take fama dashi bayan komawa birnin tarayya Abuja daga jihar Legas.

Za ku tuna cewa a watan Yuli, Aisha Buhari ta kai ziyarar ta'aziyya ga Mrs Florence Ajimobi, uwargidan tsohon gwamnan Oyo, Abiloa Ajimobi, a gidansu dake Glover Road, Ikoyi, jihar Legas.

Ajimobi ya rasu ne ranar 25 ga Yuni sakamakon jinyan da yayi bayan kamuwa da cutar Coronavirus.

Yayinda ta koma Abuja, ta killace kanta na tsawon makonni biyu saboda ciwon wuyan da take fama da shi na kimanin wata daya bayan ta'aziyyar.

Abin ya tayar da hankalin na kusa da uwargidar kuma hakan ya sa aka garzaya da ita birnin Dubai don ganin Likita.

Yanzu-yanzu: An garzaya da Aisha Buhari Dubai jinyan rashin lafiya
Yanzu-yanzu: An garzaya da Aisha Buhari Dubai jinyan rashin lafiya
Asali: Twitter

Daily Trust ta tattaro cewa Uwargidan yanzu haka tana hutawa a wani asibitin da aka sakaye sunansa amma tana cikin lafiya.

Yayinda aka tuntubi mai magana da yawunta, Aliyu Abdullahi, ya ki tsokaci kan gaskiya ko akasin haka., innama yace makonshi biyu ba ya gari.

"Ba na zuwa ofis tsawon makonni biyu. Saboda haka bai kamata in sani ba." Yace

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng