Tsohon mai tsaron baya na Super Eagles, Sofoluwe, ya riga mu gidan gaskiya
- Allah ya yi wa tsohon mai tsaron bayan kungiyar Super Eagles ta Nigeria, Yisa Sofoluwe rasuwa
- Sofuluwe ya rasu na a yammacin ranar Talata a asibitin koyarwa ta jami'ar Legas bayan jinya
- Wani daga cikin abokansa na kusa, Waidi Akanni da tsohon mai tsaron gidan Super Eagles, Dosu Joseph sun tabbatar da rasuwarsa
Tsohon mai tsaron baya na kungiyar kwallon Nigeria, Super Eagles, Yisa Sofoluwa ya rasu a ranar talata da yamma a sashin masu bukatar kulawa ta musamman na asibitin koyarwa ta jami'ar Legas.
The Punch, a ranar Juma'a ta ruwaito cewa Sofoluwe yana fama da rashin lafiya bayan gwaji ya nuna yana fama da ciwon 'mild cerebral atrophy' mai alaka da kwakwalwa.
DUBA WANNAN: Saki: Mata ta mayarwa miji sadakin N28,000 da ya biya yayin aurenta shekaru 7 da suka shude
Waidi Akanni, daya daga cikin abokan Sofoluwa na kut-da-kuta ya tabbatarwa majiyar Legit.ng rasuwarsa inda ya ce, "Sofoluwe ya tafi. Mun rasa shi yau da yamma. Allah ya jikansa. Za mu tafi asibitin ranar Laraba mu karbi gawarsa."
Dosu Joseph, tsohon mai tsaron gida na Super Eagles, shima ya tabbatar da rasuwar Sofoluwe cikin sakon WhatsApp da ya aike wa The Punch.
"Mun gode da karfafa mana gwiwa da kuke yi, mun rasa shi, wani gwarzo ya sake tafiya. Dukkan godiya ya tabbata ga Allah."
KU KARANTA: Auwalu Daudawa: Abin da yasa na mika bindigu na 20 ga gwamnatin Zamfara
An haife Sofoluwe ne a ranar 28 ga watan Disambar 1967, Sofoluwe na daga cikin tawagar Super Eagles ta Nigeria da suka kai wasar karshe na gasar AFCON ta 1984 da 1988.
Ya kuma buga wa wasu manyan kungiyoyin Nigeria da dama wasa kamar su 3SC, Abiola Babes, inda ya ci FA Cups biyu a 1985 da 1987, da Julius Berger da Gateway United.
A wani labarain daban, babban malamin Kano, Shaikh Abduljabbar Nasir Kabara ya ce rufe masallacinsa da hana shi yin wa'azo da gwamnatin jihar ta yi "zalunci ne", kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.
Malamin ya ce gwamnatin da kanta, ta bakin kwamishinan ilimi na jihar, ta tabbatar da cewa abinda ake yi masa zalunci ne amma ta dakatar da shi ba tare da bashi damar ya kare kansa ba.
Abdul-jabbar ya yi wannan jawabin ne biyo bayan rufe masallacinsa da ke makarantarsa da gwamnatin Kano ta yi a ranar Laraba gami da hana saka karuntunsa a gidajen rediyo da kafafen sada zumunta na jihar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng