Karya dokar korona: An tsare akalla mutane 200 a Kano, 25 sun tafi gidan gyara hali

Karya dokar korona: An tsare akalla mutane 200 a Kano, 25 sun tafi gidan gyara hali

- Kwamitin da ke kula da cutar korona a jihar Kano ya kama mutum sama da 200 a kokarinsa na tabbatar da bin dokokin hana yaɗuwar annobara jihar

- Daga cikin mutane 200 da aka kama an tura 25 gidan gyara hali

- Shugaban kwamitin ya tabbatar da cewa an samu mutum 102 da laifin saba doka kuma sai da aka ci tarar ko wannensu N5,000

Rahotanni sun nuna cewa kotun da ke hukunta wadanda suka karya dokar korona a jihar Kano, ta tura mutane 25 gidan gyara hali bayan ta kama su da laifi.

An tattaro cewa akalla mutane 200 jami’an tsaro suka tsare sakamakon karya dokar korona da gwamnatin jihar ta shimfida wanda daga cikinsu aka ci tarar wasu.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa Shugaba Buhari ba zai taba barin Fani-Kayode ya koma APC ba, jigon jam’iyya

Karya dokar korona: An tsare akalla mutane 200 a Kano, 25 sun tafi gidan gyara hali
Karya dokar korona: An tsare akalla mutane 200 a Kano, 25 sun tafi gidan gyara hali Hoto: Kanostate.gov.ng
Asali: UGC

Shugaban hukumar Karota, Baffa Babba DanAgundi, ya ce:

“Mun gode Allah da mutanen Kano ke bin dokar sanya takunkumin fuska domin kare lafiyarsu.

“Duk marasa bin doka da ke kin sanya takunkumin fuska za su hadu da fushin hukuma. Saboda haka dokar kariyar korona ta zauna ke nan.”

Bayan fara aiki da dokar sanya takunkumi, Gwamnatin Kano ta kafa kotun tafi-da-gidanka kimanin guda 21, wanda DanAgundi ke jagoranta.

Ya bayyan cewa an kama masu karya dokar har mutane 102 da aka ci tarar kowanensu N5,000.

Ya kara jan hankalin shugabanin kasuwanni da tabbatar da bin dokar kare kai daga annobar.

Da yake jawabi, Kwamishinan Yada Labaran jihar, Muhammad Garba ya ce sabuwar dokar za ta tabbatar da kare mutane daga kamuwa da cutar korona.

Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ta dauki matakin ne saboda yadda cutar ke kara yaduwa a jihar tun bayan sake bullarta a karo na biyu, jaridar Aminiya ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: 'Yan bindiga sun sace hadimin mataimakin gwamnan Taraba

Ya ce duk wanda kotun tafi-da-gidanka ta samu ya karya dokar to za a hukunta shi yadda doka ta tanada don haka ya ja hankalin jama’ar jihar da su kasance masu bin doka a kodayaushe.

A wani labarin kuma, Kungiyar nan ta Muslim Rights Concern watau MURIC ta yabi gwamnatin Kano a kan dakatar da Sheikh Abduljabar Nasir-Kabara daga yin wa’azi.

MURIC ta fitar da jawabi wanda shugabanta, Ishaq Akintola, ya sa hannu.Jaridar The Cable ta fitar da wannan rahoto a ranar 7 ga watan Fubrairu, 2021.

Farfesa Ishaq Akintola ya ce gwamnatin Abdullahi Ganduje ta yi maganin matsalar da wuri.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel