'Yan banga sun kama 'yan leken 'yan bindiga uku a Kaduna

'Yan banga sun kama 'yan leken 'yan bindiga uku a Kaduna

- Yan banga sun yi nasarar kama wasu mutum uku da ake zargi masu yi wa yan bindiga leken asiri ne

- Daya daga cikin wadanda ake zargin, Musa Sani, ya amsa wannan laifin inda ya kuma nemi a masa afuwa

- Tuni dai an mika su a hannun rundunar yan sandan jihar ta Kaduna domin a zurfafa bincike a kan lamarin

Yan banga na unguwa a Dutsen Abba da ke karamar hukumar Zaria sun kama wasu mutane uku da ake zargin yan leken asirin yan bindiga ne, Daily Trust ta ruwaito.

Mutane ukun da ake zargin sune Mu’azu Sani da Mubarak Adamu daga Angwar Makada; Faisal, mazaunin Angwar; da Malam Atiku na unguwar Dutsen Abba.

'Yan banga sun kama 'yan leken 'yan bindiga uku a Kaduna
'Yan banga sun kama 'yan leken 'yan bindiga uku a Kaduna. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

An gano cewa uku daga cikin wadanda ake zargin tuni an mika su hannun rundunar yan sandan jihar domin zurfafa bincike.

An kama wadanda ake zargin saboda alakarsu da yunkurin sace wasu yan gidan wani kansilar karamar hukumar Abdulazeez Sani a ranar 4 ga watan Fabrairun 2021.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun tare motar ɗaukan gawa, sun yi awon gaba da ƙanin mamacin

Daya daga cikin wadanda ake zargin, Mu'azu, cikin bidiyo da aka nada ya tabbatar da cewa yana da hannu a sace dan uwansa wato kansilar kuma ya roki a yi masa afuwa.

Kansilar, Abdulazeez Sani ya tabbatar da kama wadanda ake zargin ciki har da dan uwansa inda ya ce ana kan bincike game da lamarin.

Idan za a iya tunawa sun so sace matar kansilar, Samira Abdulazeez da wata matar aure, Halima Sani amma yan banga a Tirmi a karamar hukumar Igabi suka dakile harin kuma masu garkuwar suka tsere.

DUBA WANNAN: Hotunan hatsabibin mai garkuwa da aka kama yayin da ya tafi karbar kuɗin fansa

An kira kakakin yan sandan jihar, ASP Mohammed Jalige amma bai amsa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

A wani labarain daban, babban malamin Kano, Shaikh Abduljabbar Nasir Kabara ya ce rufe masallacinsa da hana shi yin wa'azo da gwamnatin jihar ta yi "zalunci ne", kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Malamin ya ce gwamnatin da kanta, ta bakin kwamishinan ilimi na jihar, ta tabbatar da cewa abinda ake yi masa zalunci ne amma ta dakatar da shi ba tare da bashi damar ya kare kansa ba.

Abdul-jabbar ya yi wannan jawabin ne biyo bayan rufe masallacinsa da ke makarantarsa da gwamnatin Kano ta yi a ranar Laraba gami da hana saka karuntunsa a gidajen rediyo da kafafen sada zumunta na jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel