Da duminsa: Kotu ta kwacewa matar Jonathan Naira biliyan 1

Da duminsa: Kotu ta kwacewa matar Jonathan Naira biliyan 1

Wata babbar kotun tarayyar Najeriya da ke zaman ta a jihar Kano ta bai wa hukumar nan dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC damar kwace makudan kudaden ta fiye da N1bn daga hannun matar tsohon shugaban kasa Patience Jonathan.

Sanawar da hukumar ta EFCC ta fitar ranar Alhamis din da ta gabata ta ce mai shari'a Lewis Allagoa na babbar kotun tarayyar da ke Kano ne ya bai wa hukumar izinin kwace N1,000,494,000 da kamfanin Magel Resort Limited, wanda ke da alaka da matar tsohon shugaban kasar Patience Jonathan.

Da duminsa: Kotu ta kwacewa matar Jonathan Naira biliyan 1

Da duminsa: Kotu ta kwacewa matar Jonathan Naira biliyan 1
Source: UGC

KU KARANTA: Daraktan yakin neman zaben gwamnan PDP a Gombe ya koma APC

Legit.ng Hausa ta samu haka zalika cewa tun farko dai hukumar ta EFCC ta samu bayanan sirri cewa an boye makudan kudaden ne da ba a yi amfani da su ba a bankin Fidelity a wani asusu dake da alaka da matar ta tsohon shugaban kasar, kamar dai yadda sanarwar ta bayyana.

Daga nan ne kotun ta bai wa EFCC izinin wucin gadi na kwace kudin, a cewar hukumar.

Kotun ta kuma bukaci a sanya kudin a Asusun Bai Daya na gwamnatin tarayya.

Patience Jonathan na cikin makusantan tsohon shugaban kasar, wadanda suka hada da tsofaffin ministoci da masu ba shi shawara da ake tuhuma da zarge-zargen cin hanci tun da Muhammadu Buhari ya karbi mulkin kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel