Aisha Buhari ta gana da Patience Jonathan a Aso Villa (hotuna)

Aisha Buhari ta gana da Patience Jonathan a Aso Villa (hotuna)

- Aisha Buhari ta gana da takwararta uwargidar tsohon Shugaban kasa, Dame Patience Jonthan fadar Shugaban kasa ranar Litinin, 10 ga watan Fabrairu

- Matayen shugabannin biyu sun tttauna batun gudunmawar mata a siyasar Najeriya

- Ku tuna cewa a kwanan nan ne kum Misis Buhari da takwarar tata suka hadu a wani taro don tunawa da Maryam Babangida, uwargidar tsohon Shugaban kasa a mulkin soja, Ibrahim Babangida

Uwargidar Shugaban kasar Najeriya Aisha Buhari ta gana da takwararta uwargidar tsohon Shugaban kasa, Dame Patience Jonathan fadar Shugaban kasa a ranar Litinin, 10 ga watan Fabrairu.

Uwargidar Shugaban kasr wacce ta wallafa hotunan taron a shafinta na Facebook ranar Talata, 11 ga watan Fabrairu ta yi bayanin cewa gudunmawar mata a siysa shine abunda suka tattauna a kai.

Sun kum tattauna muhimman batutuwa ciki harda ilimin yara mata da kuma aikin da Misis Jonathan ke yi mai taken chanji ga mata.

Aisha Buhari ta gana da Patience Jonathan a Aso Villa (hotuna)
Aisha Buhari ta gana da Patience Jonathan a Aso Villa
Asali: Facebook

"A jiya na karbi bakuncin uwargidar tsohon Shugaban kasa, mai girma Dame Patience Jonathan a fadar Shugaban kasa.

"Mun tattauna kokarin da nake na ganin mata sun shig harkar siyasa sosai da kuma gudunmawar mata a mulki.

Aisha Buhari ta gana da Patience Jonathan a Aso Villa (hotuna)
Aisha Buhari ta gana da Patience Jonathan a Aso Villa
Asali: Facebook

“Mun kuma tattauna ilimin yara mata da aikinta na “canji ga mata” na samu damar jin nata ra’ayin a lokacin mulkinta sannan na saurari hangenta kan lamuran da ke addabar mata da yara a kasar.

"Na ji dadin kasancewa tare da ita sosai sannan ina duba ga sake samun irin wannan zama a nan gaba,” Aisha ta wallafa a Facebook.

Aisha Buhari ta gana da Patience Jonathan a Aso Villa (hotuna)
Aisha Buhari ta gana da Patience Jonathan a Aso Villa
Asali: Facebook

Legit.ng ta lura cewa uwargidar Shugaban kasar ta kasance a sahun gaba wajen kira ga kasancewar mata a harkokin siyasa.

Aisha Buhari ta gana da Patience Jonathan a Aso Villa (hotuna)
Aisha Buhari ta gana da Patience Jonathan a Aso Villa
Asali: Facebook

Ku tuna cewa a kwanan nan ne kuma Misis Buhari da takwarar tata suka hadu a wani taro don tunawa da Maryam Babangida, uwargidar tsohon Shugaban kasa a mulkin soja, Ibrahim Babangida.

KU KARANTA KUMA: Shugabanni na tsaron fada ma Buhari gaskiya kan ta’addanci – Shehu Sani

A baya mun ji cewa aga hotunan uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da Turai Yar’adua, matar tsohon shugaban kasa marigayi Umaru Musa Yar’adua. An ga hotunan matan ne suna cikin nishadi.

Aisha Buhari ta wallafa hotunansu ne shafinta na Instagram. Ta bayyana cewa matar tsohon shugaban kasan ta kai mata ziyara ne tare da ‘ya’yanta biyu, Zainab Dakingari da Abdulaziz Yar’adua.

Kamar yadda uwargidan shugaban kasar ta bayyana, ta samu tattauna manyan lamurra da Turai. Ta ce sun tattauna a kan cin zarafin da ya danganci jinsi da kuma hanyoyin habaka matasa a Najeriya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng