Fasto zai yi zaman gidan yari bayan ya saci $90,000 da 4.5m na coci

Fasto zai yi zaman gidan yari bayan ya saci $90,000 da 4.5m na coci

- Wata kotu ta laifuka na musamman dake jihar Legas ta yankewa wani fasto shekaru 3 a gidan yari bisa laifin satar kudaden coci

- An yanke hukuncin ne bayan kotu ta tabbatar da yadda Afolabi Samuel ya lallaba ya sace $90,000 da N4,500,000 wanda aka tara saboda yi wa addini hidima

- EFCC ta mika Samuel, wanda shine ma'aji kuma akawun cocin gaban alkali Mojisola Dada bisa laifuka biyu, sata da almundana gami da ha'inci

Kotun jihar Legas ta laifuka na musamman dake Ikeja ta yanke wa faston Living Faith Church wacce aka fi sani da Winner's Chapel, Afolabi Samuel, shekaru 3 a gidan gyaran hali bisa satar $90,000 da N4,500,000 wanda 'yan coci suka hada karfi da karfe suka tara.

EFCC ta gabatar da Samuel wanda shine akawu kuma ma'ajin cocin gaban alkali Mojisola Dada bisa laifuka biyu, almundahana da sata.

Kamar yadda EFCC ta gabatar, faston da wata Blessing Kolawole, wacce take aiki a jami'ar Covenant, sun hada kulle-kullen satar dukiyar kuma sun sake a aljihunansu don amfaninsu.

Fasto zai yi zaman gidan yari bayan ya saci $90,000 da 4.5m na coci
Fasto zai yi zaman gidan yari bayan ya saci $90,000 da 4.5m na coci. Hoto daga @MobilePunch
Source: Twitter

KU KARANTA: Karamar yarinyar da ta damki hannun Osinbajo a tsakar kasuwar Nyanya ta zama 'diyarsa'

Hukumar ta zargi Samuel, wanda cocin ta dauka musamman don kulawa da shige da ficen kudade, inda yayi amfani da matsayinsa suka hada kai da wasu suka yi ta satar dukiyoyin al'umma.

Laifukan sun yi karantsaye da bangarori na 278, 285 da 490 na dokar masu laifi na jihar Legas No. 11, 2011.

Lauyan Samuel ya lura da yadda laifinsa ya zubar da mutuncinsa da na iyayensa, don haka ya roki kotu tayi adalci tare da ragwame, Punch ta wallafa.

Ogunwuyi ya ce ya amsa laifinsa, kuma Samuel ya yi amfani da kudaden ne wurin biya wa yaransa kudin makaranta da kulawa da tsofaffin iyayensa.

Alkalin ya ci shi tarar N1,000,000 sannan ya umarce shi da ya mayar da $90,000 da kuma N2,358,000 zuwa cocin.

KU KARANTA: Kwamandojin ISWAP Sulum da Borzogo sun sha da kyar, soji sun kwace sansaninsu a Timbuktu

A wani labari na daban, sabbin dalilai sun bayyana a kan abinda yasa jigon jam'iyyar APC Asiwaju Bola Tinubu da kuma uban jam'iyya, Bisi Akande da wasu suke sukar sabunta rijistar da 'yan jam'iyyar ke yi a kasar nan.

Fiye da dalilan da shugabannin biyu suka sanar, majiyoyi da suke tattare da su sun ce zargin wani mugun abu zai bullo daga shugabannin jam'iyyar na yanzu sune sahihan dalilan da suka sa Akande da Tinubu suke sukar rijistar.

Kwamitin rikon kwarya da tsari na jam'iyyar karkashin shugabancin Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya fara rijistar 'yan jam'iyyar a fadin kasar nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel