Ba za a iya jan ra'ayinmu don tabbatar da nadin da aka yi wa tsoffin hafsoshin tsaro ba, Majalisa

Ba za a iya jan ra'ayinmu don tabbatar da nadin da aka yi wa tsoffin hafsoshin tsaro ba, Majalisa

- Majalisar dattawan Najeriya ta ce babu wani abu da za a iya mata domin jan ra'ayinta wurin tabbatar da nadin da aka yi wa tsoffin hafsoshin tsaro

- Kakakin majalisar, Sanata Basiru Ajibola ya ce za su tabbatar da nadin ne matukar sun cancanta ba tare da wani batun tirsasawa ba

- Tsohon sakataren hulda da jama'a na APC ya zargi cewa za a bai wa kowanne sanata $100,000 kafin a tabbatar da nadin

A jiya ne majalisar dattawa ta bayyana cewa babu abinda zai sa a tirsasa ta tantance tare da tabbatar da nadin da shugaba Buhari yayi wa tsoffin hafsoshin tsaro.

A makon da ya gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika wa majalisar dattawa sunayen tsoffin hafsoshin tsaro a matsayin jakadu.

A yayin da kungiyar Yarabawa, Afenifere tace majalisar za ta iya tabbatar da tsoffin shugabannin tsaron amma bai dace shugaban kasan yayi wannan nadin ba.

KU KARANTA: Ayyukanku suna kamanceceniya da na 'yan Boko Haram, Garba Shehu ga PDP

Ba za iya jan ra'ayinmu domin tabbatar da nadin da aka yi wa tsoffin hafsoshin tsaro ba, Majalisa
Ba za iya jan ra'ayinmu domin tabbatar da nadin da aka yi wa tsoffin hafsoshin tsaro ba, Majalisa. Hoto daga @Vanguardngrnews
Source: Twitter

Amma tsohon sakataren hulda da jama'a na jam'iyyar mai mulki, Timi Frank a wata takarda da ya fitar ya zargi cewa akwai wani shiri na bai wa kowanne sanata $100,000 domin tabbatar da nadin.

Sai dai kakakin majalisar dattawan, Sanata Ajibola Basiru a wata tattaunawa da aka yi da shi a THISDAY ya musanta wannan zargin.

Ya bayyana cewa majalisar za ta tabbatar da nadin matukar sun cacanta ba tare da wani ya juya ra'ayoyinsu ba.

Basiru yayi kira ga abokan aikinsa da sauran jama'a da kada su dauka wannan zargin ballantana abu ne da yake fitowa daga bakin Frank.

Ya ce: "A baya ya saba bayyana manyan zargi wadanda ba gaskiya bane. babu mai hankalin da ya dace ya karba zantukansa da muhimmanci."

KU KARANTA: Miloniyoyin Najeriya 5 masu karancin shekaru a 2021 da yadda suka tara dukiyarsu

A wani labari na daban, babban malami mazaunin jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta yi amfani da kasafin kudin da ta ware domin yaki da ta'addancin da ke mamaye arewa.

Gumi, wanda ya yi magana a cigaban ziyarar kwana biyar da ya kai wa Fulani a jihar Zamfara, ya ce manyan kudaden da ake warewa wurin tsaron kasar nan kamata yayi a yi amfani da su wurin shawo kan matsalar Fulani.

"Wadannan biliyoyin sun isa har sun yi yawa wurin shawo kan bukatun Fulani wanda ya hada da kayan more rayuwa, horar da su tare da samar musu da jari," ya kara da cewa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel