Kwamandojin ISWAP Sulum da Borzogo sun sha da kyar, soji sun kwace sansaninsu a Timbuktu

Kwamandojin ISWAP Sulum da Borzogo sun sha da kyar, soji sun kwace sansaninsu a Timbuktu

- Rundunar sojin kasa da na sama sun samu nasarar mamaye sansanin mayakan ISWAP

- Sun samu nasarar kashe kwamandojinsu guda 2 Modu Sulum da Modu Borzogo sun sha da kyar

- Rundunar ta kwace yankin Tumbuktu wanda ya kasance a hannun 'yan Boko Haram tun a 2013

Rundunar sojin kasa da na sama sun samu nasarar mamaye sansanin mayakan IS, inda suka kashe manyan kwamandojinsu sauran kuma suka ranta a na kare, kamar yadda majiyoyin soji guda biyu suka sanar da AFP a ranar Alhamis.

Mayakan ISWAP dake da sansani a wuraren Yobe da jihar Borno a arewa maso gabas sun sha ragargaza hannun sojojin Najeriya, arise tv ta wallafa.

Wannan nasarar ta biyo bayan shugaba Muhammadu Buhari ya sauya hafsoshin sojin Najeriya guda 4 bayan an yi watanni ana matsa masa da ya canja su saboda sun gaza samar da zaman lafiya a kasa.

KU KARANTA: A yi amfani da kasafin tsaro wurin shawo kan matsalar 'yan bindiga, Gumi ya shawarci FG

Kwamandojin ISWAP Sulum da Borzogo sun sha da kyar, soji sun kwace sansaninsu a Timbuktu
Kwamandojin ISWAP Sulum da Borzogo sun sha da kyar, soji sun kwace sansaninsu a Timbuktu. Hoto daga arise.tv
Asali: UGC

A ranar Laraba, sojojin suka hada guiwa da mayakan sama inda suka yi kaca-kaca da wurin da 'yan ta'addan suke kira "Timbuktu triangle", kamar yadda sojojin suka tabbatar.

Dama tun 2013 'yan ta'addan suka mamaye wurin, inda suke cin karensu babu babbaka, musamman wuraren Talala, wanda wurin shine sansanin ISWAP na biyu a girma.

A watan da ya gabata rundunar soji ta kai wa 'yan ta'addan dake Talala farmaki inda wani mai kunar bakin wake yayi sanadiyyar mutuwar sojoji 6.

Manyan kwamandojin ISWAP, Modu Sulum da Ameer Modu Borzogo sun tsere tare da wasu mayakan sakamakon ruwan wutar da suka ji, majiya ta biyu ta tabbatar.

KU KARANTA: Hotunan kafin aure na matashin da zai yi wuff da kyawawan 'yan mata 2 a rana daya a Abuja

A wani labari na daban, shugaban majalisar sarakunan jihar Zamfara kuma Sarkin Anka, Alhaji Attahiru Muhammad Ahmed ya ja kunne a kan auren mace fiye da daya wanda yayi ikirarin shine dalilin tabarbarewar ilimi a kasar nan.

A yayin magana a taron sarakunan jihar 17 da shugaban UBE na jihar Zamfara, Alhaji Abubakar Aliyu Maradun a Gusau, Sarkin Anka wanda ya fara alakanta talauci da tara mata, yayi kira ga al'ummar Musulmi da su tabbatar da sun bai wa 'ya'yansu ilimi na boko da zamani mai nagarta.

Basaraken ya jaddada goyon bayan sarakunan gargajiya ga ilimin zamani a jihar Zamfara da jama'arta baki daya, Linda Ikeji ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: