Karamar yarinyar da ta damki hannun Osinbajo a tsakar kasuwar Nyanya ta zama 'diyarsa'

Karamar yarinyar da ta damki hannun Osinbajo a tsakar kasuwar Nyanya ta zama 'diyarsa'

- Mai hoton mataimakin shugaban kasan Najeriya, farfesa Osinbajo, ya yi wata wallafa mai cike da tarihi a ranar Asabar, 6 ga watan Fabrairu

- Tolani Alli, ya wallafa wasu hotunan yarinyar da ta cafki hannun Osinbajo a kasuwa tana kiran shi ya ga shagonsu

- A halin yanzu tana fadar shugaban kasa inda take zama da mahaifiyarta kuma tana jami'a tana karatun likitanci

Tolani Alli, mai hoton farfesa Yemi Osinbajo na musamman ya wallafa hotunan wata yarinya mai suna Chinaza mai cike da tarihi a ranar Asabar, 6 ga watan Fabrairu.

A cewar Tolani, Chinaza ta bangaje mai bai wa mataimakin shigaban kasa tsaro ta gudu ta damki hannun Osinbajo tana rokon yaje ya kai wa shagon mahaifiyarta ziyara.

Lamarin ya faru ne a kasuwar Nyanya dake birnin tarayya, Abuja lokacin da Osinbajo yake kokarin bunkasa arzikin kananun tiredodi.

Karamar yarinyar da ta damki hannun Osinbajo a tsakar kasuwar Nyanya ta zama 'diyarsa'
Karamar yarinyar da ta damki hannun Osinbajo a tsakar kasuwar Nyanya ta zama 'diyarsa'. Hoto daga @tolanialli
Source: Twitter

KU KARANTA: Kakakin majalisar Kwara ya sallami hadiminsa saboda ya ceci dan APC da aka kaiwa hari

Osinbajo ya zagaye manyan kasuwanni lokacin da suka kaddamar da shirin TraderMoni don tabbatar da cewa tiredodi sun samu kudaden.

Bayan ya je kasuwar ne Chinaza ta isa wurinsa, inda tace tana so yazo yaga shagon mahaifiyarta saboda ta fara sana'ar ne bayan ta samu kaimin fara sana'ar bayan ganinsa a talabijin da sauran kafafen yada labarai.

Bayan shekaru 2 da faruwar haka ne sai ga Chinaza da mahaifiyarta a fadar shugaban kasa zaune da wanda ya dauki nauyinta kamar diyarsa.

Bayan shekaru 3 da faruwar haka aka gano cewa Chinaza tana jami'a tana shirin zama likita kuma ta samu karfin guiwan yin hakan ne daga farfesa Osinbajo.

KU KARANTA: A yi amfani da kasafin tsaro wurin shawo kan matsalar 'yan bindiga, Gumi ya shawarci FG

A wani labari na daban, shugaban majalisar sarakunan jihar Zamfara kuma Sarkin Anka, Alhaji Attahiru Muhammad Ahmed ya ja kunne a kan auren mace fiye da daya wanda yayi ikirarin shine dalilin tabarbarewar ilimi a kasar nan.

A yayin magana a taron sarakunan jihar 17 da shugaban UBE na jihar Zamfara, Alhaji Abubakar Aliyu Maradun a Gusau, Sarkin Anka wanda ya fara alakanta talauci da tara mata, yayi kira ga al'ummar Musulmi da su tabbatar da sun bai wa 'ya'yansu ilimi na boko da zamani mai nagarta.

Basaraken ya jaddada goyon bayan sarakunan gargajiya ga ilimin zamani a jihar Zamfara da jama'arta baki daya, Linda Ikeji ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel