Zaman sulhu: Maganar da shugaban ƴan bindiga na Zamfara ya faɗa mun - Gwamna Matawalle

Zaman sulhu: Maganar da shugaban ƴan bindiga na Zamfara ya faɗa mun - Gwamna Matawalle

- Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya ce wani shugaban yan bindiga ya taba jan hankalinsa kan wani batu yayinda suke tattaunawa don sulhu

- Ya ce shugaban yan bindigan ya nemi da a daina yadawa a duk lokacin da jami'an tsaro suka kama yan bindiga

- A cewar dan bindigan, shugabanninsu na amfani da hakan wajen shawo kan wadanda ke da niyar mika wuya daga aikata hakan

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, a ranar Talata, 6 ga watan Oktoba, ya ce wani shugaban yan bindiga ya taba rokonsa a yayin wata ganawa, cewa a daina yadawa idan jami’an tsaro suka kama su.

Matawalle ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar radiyo da talbijin na RATTAWU, karkashin jagorancin shugabansu, Dr Kabir Garba Tsanni a Gusau.

Ya ce, a yayin ganawar, daya daga cikin shugabannin ya ce masa: “Yallabai, ina so na ja hankalinka ga wani abu mai muhimmanci, idan kana so ka samu nasara na kaso 80 a kokarin da kake yi na dawo da zaman lafiya a jihar, toh ka daina baza hotunan yan bindigan da jami’an tsaro suka kama a bainar jama’a.

“Dalilin da yasa na fada maka haka shine cewa manyan shugabanninmu na amfani da batun yada wadanda aka kama wajen shawo kan wadanda ke da niyan mika wuya da komawa cikin gari don fara sabuwar rayuwa. Suna nuna masu hakan a matsayin tozarci,” in ji shi.

Zaman sulhu: Maganar da shugaban ƴan bindiga na Zamfara ya faɗa mun - Gwamna Matawalle
Zaman sulhu: Maganar da shugaban ƴan bindiga na Zamfara ya faɗa mun - Gwamna Matawalle Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Daga nan Matawalle ya bukaci kafofin watsa labarai da su dunga kawo rahoton abubuwa ta bangaren da suke da kyau.

KU KARANTA KUMA: Sokoto: An gurfanar da matashin da ya baza bidiyon tsiraicin wata budurwa gabannin bikinta

Ya ce kafofin watsa labarai na da muhimmin rawa da za su taka wajen sanya tunani mai kyau a zukatan al’umma, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

“Wadanda ke dakile kokarinmu na dawo da zaman lafiya saboda suna jam’iyyar mai mulki su sauya tunani.

“Ba za mu nade hannuwanmu mu zuba wa wasu ido su bata kokarinmu na dawo da doka da Odar ba,” gwamnan ya yi gargadi.

A nashi martanin, shugaban RATTAWU, Dr Kabir Garba, ya ce sun yaba da nasarorin da gwamnatin Matawalle ta samu wajen dawo da zaman lafiya a jihar ta hanyar yin sulhu.

KU KARANTA KUMA: Mun warware matsalar jam'yyar APC a jihohi 11 - Mai Mala Buni

A wani labarin, gwamna Matawalle ya bayyana yadda gwamnatinsa ta tanadi zinari mai kimar Naira Biliyan 5 ga abokan kasuwancinsu na kasar waje.

Zailani Bappa, mai bai wa gwamnan shawara akan yada labarai, ya bayyana hakan ga manema labarai a wata takarda a Gusau, babban birnin jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel