Ayyukanku suna kamanceceniya da na 'yan Boko Haram, Garba Shehu ga PDP

Ayyukanku suna kamanceceniya da na 'yan Boko Haram, Garba Shehu ga PDP

- Fadar shugaban kasa ta zargi jam'iyyar adawa ta PDP da yin ayyuka masu kama da na 'yan Boko Haram

- Hadimin Buhari na musamman, Garba Shehu ne ya caccaki PDP akan kalubalantar nadin da Buhari ya yi wa tsoffin hafsoshin tsaro

- Dama jam'iyyar PDP ta dade tana zargin tsofaffin hafsoshin da rashin jajircewa wurin yaki da ta'addanci

Fadar shugaban kasa ta zargi jam'iyyar PDP da yin ayyuka masu kama da na Boko Haram. A wata takarda da hadimin Buhari na musamman akan yada labarai, Garba Shehu, ya saki, fadar shugaban kasa ta caccaki jam'iyyar PDP saboda kin amincewa da nadin tsofaffin hafsoshin sojin Najeriya mukami.

Kola Ologbondigan, sakataren PDP na kasa, ya bayyana nada tsofaffin hafsoshin sojin Najeriya a matsayin jakadun Najeriya a kasashen ketare a matsayin abinda bai dace ba, kuma ya bukaci kada 'yan majalisar dattawa ta amince da hakan.

Ayyukanku suna kamanceceniya da na 'yan Boko Haram, Garba Shehu ga PDP
Ayyukanku suna kamanceceniya da na 'yan Boko Haram, Garba Shehu ga PDP. Hoto daga guardian.ng
Source: UGC

Sai dai Shehu ya ce an nada su ne saboda jajircewarsu da dagewarsu akan Najeriya, Daily Trust ta wallafa.

KU KARANTA: A yi amfani da kasafin tsaro wurin shawo kan matsalar 'yan bindiga, Gumi ya shawarci FG

"Shugaban kasa yana kokarin kyautata musu saboda aiki tukuru da suka yi wa kasar nan, kuma ba za a taba mantawa dasu ba, ko ba jima ko ba dade. Za a basu damar samun cigaba. Wannan ne zai bai wa duk wani mai burin dagewa ya kara zage damtsensa.

"Sai dai gidajen jaridu dake yanar gizo cike suke da wallafa iri-iri wasu masu ban dariya wasu kuma na gutsiri tsoma akan tsofaffin hafsoshin sojin.

"A dage wurin yi wa wata makauniyar jam'iyya addu'a, wacce bata yi wa kasa fatan alheri, wacce take caccakar masu burin kawar da 'yan ta'addan Boko Haram. Ayyukan 'yan Boko Haram ne jam'iyyar PDP take yi, to mai ya rage wa 'yan Boko Haram?," yace.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun aika mutum 2 lahira, jami'an tsaro sun ceto mutum 19 a Kaduna

A wani labari na daban, kakakin majalisar jihar Kwara, Salihu Danladi, ya sallami hadiminsa na harkar yada labarai, Ibrahim Sheriff, a kan rawar da ya taka yayin rikicin da aka samu a taron mambobin jam'iyyar APC a Ilorin a ranar Talata.

Sheriff ya ce an sallame shi ne saboda ya ceci tsohon shugaban jam'iyyar APC na jihar, Bashir Bolarinwa daga farmakin da wata mata mai goyon bayan Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ta kai masa yayin da ake taron.

Premium Times ta wallafa yadda rikici ya barke a wani dakin taro da ke gidan gwamnatin jihar Kwara inda ake taron kafin a fara rijistar 'yan jam'iyyar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel