Gwamnatin Kano ta karyata batun rusa makarantar Sheikh Abduljabbar Kabara

Gwamnatin Kano ta karyata batun rusa makarantar Sheikh Abduljabbar Kabara

- Gwamnatin Ganduje ta musanta batun rushe makarantar da Sheikh Abdul jabbar Nasiru Kabara ke yi wa dalibansa karatu

- Ta ce gine-ginen da aka rusa dai suna kusa da wajen da malamin ke bayar da karatu amma ba nasa bane

- kakakin hukumar tsara muhalli ta jihar Kano, Ado Muhammad Gama ya bayar da tabbacin cewa makarantar malamin na nan babu abunda ya same ta

Gwamnatin jihar Kano ta karyata batun rushe ginin makarantar Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara da ke birnin jihar.

Kakakin hukumar tsara muhalli ta jihar Kano wato KANUPDA, Ado Muhammad Gama, ya sanar da sashin Hausa na BBC cewa gine-ginen da aka rusa suna kusa da wajen da malamin ke bayar da karatu amma ba nasa ba ne.

KU KARANTA KUMA: Kano ta amince da naira miliyan 245 domin yin auren mata da yawa

Gwamnatin Kano ta karyata batun rusa makarantar Sheikh Abduljabbar Kabara
Gwamnatin Kano ta karyata batun rusa makarantar Sheikh Abduljabbar Kabara Hoto: @Tvcnewsng
Source: Twitter

Ya ce:

"Su gine-ginen da ake magana a kai, wasu mutane ne suka yi su ba bisa ka'ida ba shi ya sa yanzu muka rusa su.

"A baya, Sheikh Abdujjabbar ya kasance daga cikin mutane sama da dubu da suka zo hukumarmu suka ce filin nasu ne amma sun kasa kawo hujja.

“An bukaci mutanen da suka yi ginin a kan kada su soma shi amma sai suka yi burus shi ya sa aka rusa.”

Ya kuma tabbatar da cewar makarantar Sheikh Abduljabbar tana nan babu abin da ya same ta.

KU KARANTA KUMA: Rikicin APC a Kwara: An kwantar da jiga-jigan jam’iyyar 5 bayan musayar naushi da jefe-jefen kujeru da suka yi

A gefe guda mun ji a baya cewa gwamnatin jihar Kano ta rushe makarantar da da Sheikh Abdul jabbar Nasiru Kabara ke yi wa dalibansa karatu a kusa da Jauful-Fara da ke filin mushe a Kano, kamar yadda BBC ta ruwaito.

An dade ana dauki ba dadi game da filin tsakanin shaihin malamin da al'ummar unguwar ta filin mushe inda Shaikh Abdul Jabbar ke karatu.

Gwamnatin Kano ta kwace filin ne biyo bayan korafi da ta samu daga mazauna yankin inda suka ce sune suka mallaki filin ba malamin ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel