Sanata Kabiru Gaya ya sha ihu a gaban manyan APC (Bidiyo)

Sanata Kabiru Gaya ya sha ihu a gaban manyan APC (Bidiyo)

Mun samu labari cewa Sanata Kabiru Gaya ya ji kunya wajen wani taro na Jam’iyyar APC mai mulki da aka yi kwanaki inda aka karbi tsohon Gwamna Malam Ibrahim Shekarau daga PDP zuwa APC a Kano.

Sanata Kabiru Gaya ya sha ihu a gaban manyan APC (Bidiyo)
Ganduje tare da Shekarau da Shugaban APC a Jihar Kano
Asali: Depositphotos

A makon da ya wuce ne tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau ya fice daga Jam’iyyar PDP ya dawo Jam’iyyar APC. A dalilin haka ne Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Adams Oshimhole da wasu manyan Jam'iyyar su ka je gidan tsohon Gwamnan.

Kamar yadda labari ya zo mana, manyan ‘Yan siyasar Kano su na wajen wannan taro da aka yi. Sanatocin Jihar irin su Barau Jibril da Kabiru Gaya da kuma wasu ‘Yan Majalisa sun halarci zaman da aka yi da tsohon Gwamna Shekarau da sauya sheka.

A lokacin da ake gabatar da ‘Yan siyasar na APC, jama’a sun yi ta tafi su na jinjina masu. Sai dai lokacin da aka zo kan Sanata Kabir Gaya wanda ke wakiltar Kano ta Kudu a Majalisar Dattawa, wasu sun yi masa ihu har ta kai manyan APC sun sa baki a wurin.

KU KARANTA: 'Yan adawa ne kar zargin Buhari da cin hanci - Garba Shehu

Shugaban APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas sai da ya zagi wadanda su ka yi wa babban Sanatan ihun ba su yi a wajen taron. Wasu sun nuna cewa ba su tare da Sanatan inda su ke neman Jam’iyyar ta tsaida Kawu Sumaila a matsayin Sanatan Kudancin Kano.

Kun samu labari cewa yayin da tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau ya fice daga Jam’iyyar PDP zuwa APC mai mulki, Shugabannin Jam’iyyar PDP da wasu manyan ‘Yan siyasar Kano sun nuna goyon-bayan su ga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Jama'a su na yi wa Kabiru Gaya ihu a gaban Gwamna Ganduje da sauran manyan Jam'iyya

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng