Auren mace fiye da 1 na da nasaba da tabarbarewar ilimi a kasar nan, Sarkin Anka

Auren mace fiye da 1 na da nasaba da tabarbarewar ilimi a kasar nan, Sarkin Anka

- Shugaban majalisar sarakunan Zamfara kuma sarkin Anka, ya alakanta tabarbarewar ilimi da auren mace fiye da daya

- Alhaji Attahiru Muhammad Ahmed ya ja kunnen maza a kan auren mace fiye da daya saboda hakan ke hana a samu ilimi mai nagarta

- Ya bayyana hakan ne a taronsa da sarakuna 17 na jihar Zamfara tare da shugaban hukumar UBE ta jihar baki daya

Shugaban majalisar sarakunan jihar Zamfara kuma Sarkin Anka, Alhaji Attahiru Muhammad Ahmed ya ja kunne a kan auren mace fiye da daya wanda yayi ikirarin shine dalilin tabarbarewar ilimi a kasar nan.

A yayin magana a taron sarakunan jihar 17 da shugaban UBE na jihar Zamfara, Alhaji Abubakar Aliyu Maradun a Gusau, Sarkin Anka wanda ya fara alakanta talauci da tara mata, yayi kira ga al'ummar Musulmi da su tabbatar da sun bai wa 'ya'yansu ilimi na boko da zamani mai nagarta.

Basaraken ya jaddada goyon bayan sarakunan gargajiya ga ilimin zamani a jihar Zamfara da jama'arta baki daya, Linda Ikeji ta wallafa.

KU KARANTA: Mutum 6 sun sheka lahira, 6 sun jigata bayan hatsarin da 'yan bindiga suka haddasa a titin Birnin Gwari

Auren mace fiye da 1 na da nasaba da tabarbarewar ilimi a kasar nan, Sarkin Anka
Auren mace fiye da 1 na da nasaba da tabarbarewar ilimi a kasar nan, Sarkin Anka. Hoto daga @Lindaikeji
Source: Twitter

KU KARANTA: Bidiyon wanda ake zargi yana nuna soyayyarsa ga kyakyawar alkalin da take masa shari'a

A wani labari na daban, kakakin majalisar jihar Kwara, Salihu Danladi, ya sallami hadiminsa na harkar yada labarai, Ibrahim Sheriff, a kan rawar da ya taka yayin rikicin da aka samu a taron mambobin jam'iyyar APC a Ilorin a ranar Talata.

Sheriff ya ce an sallame shi ne saboda ya ceci tsohon shugaban jam'iyyar APC na jihar, Bashir Bolarinwa daga farmakin da wata mata mai goyon bayan Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ta kai masa yayin da ake taron.

Premium Times ta wallafa yadda rikici ya barke a wani dakin taro da ke gidan gwamnatin jihar Kwara inda ake taron kafin a fara rijistar 'yan jam'iyyar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel