Kakakin majalisar Kwara ya sallami hadiminsa saboda ya ceci dan APC da aka kaiwa hari

Kakakin majalisar Kwara ya sallami hadiminsa saboda ya ceci dan APC da aka kaiwa hari

- Kakakin majalisar Kwara, Salihu Danladi ya sallami hadiminsa na yada labarai a kan ya taimaki tsohon shugaban APC Bolarinwa

- Sheriff ya ce ya ceci Bolarinwa ne yayin da wata mai goyon bayan Gwamna AbdulRazaq ta kai masa hari yayin da ake taron jam'iyyar

- An gano cewa an samu baraka a jam'iyyar APC ta Kwara tsakanin gwamnan jihar da wasu shugabannin da Lai Mohammed yake jagora

Kakakin majalisar jihar Kwara, Salihu Danladi, ya sallami hadiminsa na harkar yada labarai, Ibrahim Sheriff, a kan rawar da ya taka yayin rikicin da aka samu a taron mambobin jam'iyyar APC a Ilorin a ranar Talata.

Sheriff ya ce an sallame shi ne saboda ya ceci tsohon shugaban jam'iyyar APC na jihar, Bashir Bolarinwa daga farmakin da wata mata mai goyon bayan Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ta kai masa yayin da ake taron.

Premium Times ta wallafa yadda rikici ya barke a wani dakin taro da ke gidan gwamnatin jihar Kwara inda ake taron kafin a fara rijistar 'yan jam'iyyar.

KU KARANTA: Bidiyon wanda ake zargi yana nuna soyayyarsa ga kyakyawar alkalin da take masa shari'a

Kakakin majalisar Kwara ya sallami hadiminsa saboda ya ceci dan APC da aka kaiwa hari
Kakakin majalisar Kwara ya sallami hadiminsa saboda ya ceci dan APC da aka kaiwa hari. Hoto daga @Premiumtimes
Asali: Twitter

Kwamitin rijista na jam'iyyar APC ya bukaci a yi taron saboda a jaddada zaman lafiya ganin yadda jam'iyyar ta fada rikici a Kwara wanda ke kara tsananta sakamakon tsige Bolarinwa da aka yi.

Wannan cigaban ya faru ne sakamakon barakar da aka samu tsakanin Gwamna AbdulRazaq da wata kungiyar shugabannin jam'iyyar wacce ta samu jagorancin ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed.

Duk da shugabannin jam'iyyar na kasa da shugabannin arewa ta tsakiya sun shiga lamarin, babu wani cigaba da ya samu.

KU KARANTA: Gwamnonin arewa sun yi magana da kakkausar murya a kan harin da ake kaiwa makiyaya

A wani labari na daban, wasu 'yan bindiga sun kutsa wata coci inda suka halaka wani mutum mai matsakaicin shekaru mai suna Ken Ekwesianya, matarsa da diyarsu a Azia da ke karamar hukumar ihiala ta jihar Anambra.

Kamar yadda majiya ta tabbatar, wanda aka kashen an halaka shi ne a farfajiyar cocin wurin karfe 7 na yammacin ranar Alhamis, Daily Trust ta wallafa.

Har a halin yanzu babu gamsasshen bayani game da lamarin amma kakakin rundunar 'yan sandan na jihar, Haruna Mohammed, ya tabbatar da aukuwar lamarin kuma ya ce ana cigaba da bincike.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: