Bidiyon wanda ake zargi yana nuna soyayyarsa ga kyakyawar alkalin da take masa shari'a
- Wani wanda ake zargi ya bai wa jama'a mamaki bayan ya yi tunanin soyayya za ta tseratar da shi daga hukunci
- Demeritus Lewis ya nemi wuce makadi da rawa inda ya mika tayin soyayyarsa ga alkalin da ke masa shari'a
- Kyakyawar alkalin da ke shari'ar ta sanar da wanda ake zargin cewa fasa mata kai ba zai tseratar da shi ba
Wani da ake zargin barawo ne a Florida mai suna Demetrius Lewis ya mika kokon bararsa ga alkali mace yayin da ake zaman kotuun ta yanar gizo a ranar Alhamis, 4 ga watan Fabrairu.
A yayin zaman kotun, matashin ya sanar da alkalin yadda take da kyau tare da sanar da ita cewa yana matukar son ta.
Alkalin mai suna Tabitha Blackmon ta yi murmushi sannan ta sanar da wanda ake zargin cewa yabonta ba zai yi aiki a kotu ba.
KU KARANTA: Gwamnonin arewa sun yi magana da kakkausar murya a kan harin da ake kaiwa makiyaya
Wanda ake zargin ya ce: "Alkali, kina da kyau, ke kyakyawa ce. Dole ne in sanar da ke kina da kyau. Ina son ki. Ina matukar son ki."
Cike da kwarewa alkalin ta yi masa martani da: "Yauwa Lewis. Yabona ko fasa min kai ba zai kai ka ko ina ba, kila ba a nan ba."
Ana zargin Lewis da fasa wani gida tare da shiga yayi sata sannan kuma ya mallaki miyagun kwayoyi.
Bayan shafin Linda Ikeji ya wallafa wannan bidiyon, jama'a da dama sun dinga tsokaci daban-daban tare da bayyana tunaninsu.
KU KARANTA: Jami'an tsaro da farin kaya sun cafke Nastura da wasu jiga-jigan CNG a Kaduna
A wani labari na daban, Fasto Tunde Bakare, mai kulawa da cocin Citadel Global Community, wanda a baya ake kiranshi da Latter Rain Assembly, ya musanta ikirarin cewa Buhari ya ci amanar 'yan Najeriya a ranar Alhamis.
Ya kuma bayyana ra'ayinsa akan yadda Sunday Igboho ya shiga al'amarin kisan makiyaya, Vanguard ta wallafa.
Faston ya yi wannan musun ne a Arise TV, bayan an tambaye shi akan hirarsa da mawallafin Ovation Magazine, Dele Momodu, a Instagram.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng