Gwamnatin Kano ta rusa makarantar Sheikh Abduljabbar Kabara

Gwamnatin Kano ta rusa makarantar Sheikh Abduljabbar Kabara

- Gwamnatin jihar Kano ta rusa makarantar da Sheikh Abdul jabbar ke koyarwa a Kano

- Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin jihar ta haramtawa malamin cigaba da karatu a jihar

- Dama dai an dade ana rikici game da filin da makarantar ya ke tsakanin malamin da mutanen unguwa

Gwamnatin jihar Kano ta rushe makarantar da da Sheikh Abdul jabbar Nasiru Kabara ke yi wa dalibansa karatu a kusa da Jauful-Fara da ke filin mushe a Kano, kamar yadda BBC ta ruwaito.

An dade ana dauki ba dadi game da filin tsakanin shaihin malamin da al'ummar unguwar ta filin mushe inda Shaikh Abdul Jabbar ke karatu.

Gwamnatin Kano ta rusa makarantar Sheikh Abduljabbar Kabara
Gwamnatin Kano ta rusa makarantar Sheikh Abduljabbar Kabara. Hoto: @Tvcnewsng
Source: Twitter

Gwamnatin Kano ta kwace filin ne biyo bayan korafi da ta samu daga mazauna yankin inda suka ce sune suka mallaki filin ba malamin ba.

DUBA WANNAN: Gwamna Bala Mohammed: Yadda na kusa rasa aiki na saboda Jami'ar Baze

A kalla watanni biyu da suka gabata kenan da gwamnati ta fitar da filaye a wajen ciki har da na Shaikh Abdul jabbar da ya yi ikirarin cewa gwamnatin da ta gabata ne ta ba shi filin.

Tun a farkon wannan makon dai gwamnatin na jihar Kano bayan zaman majalisar zartarwa na jihar ta haramta wa malamin yin karatu ko huduba a jihar sannan ta hana gidajen rediyo da talabijin saka karatunsa.

Gwamnatin ta ce ta dauki wannan matakin ne biyo bayan korafe-korafe da aka shigar a kansa na zargin cewa yana yi wa sahabai batanci, zargin da malamin ya musanta.

A bangarensa, malamin ya ce abinda gwamnatin Kano ta yi masa ba komi bane illa 'zalunci' inda ya ce ba ta gayyace shi ta ba shi damar ya yi magana ya kare kansa ba.

KU KARANTA: Ba makiyaya bane suka bankawa makarantar sakandare wuta, Gwamnatin Kogi

Bayan wannan matakin dakatarwa, Shaikh Abdul jabbar ya ce zai mayar da hankalinsa wurin yin rubuce-rubuce wanda ya ce za su hana wadda suka yi dalilin dakatar da shi yin barci.

Malamin kuma ya yi ikirarin cewa gwamna Abdullahi Ganduje na Kano yana masa bita da kulli ne saboda bai goyi bayansa ba a zaben gwamna na jihar da ta gabata.

Sai dai Ganduje ya musanta wannan zargin inda ya ce babu batun siyasa a cikin dakatar da malamin sai dai kawai magana ce ta tabbatar da zaman lafiya a jihar.

A wani labarain daban, babban malamin Kano, Shaikh Abduljabbar Nasir Kabara ya ce rufe masallacinsa da hana shi yin wa'azo da gwamnatin jihar ta yi "zalunci ne", kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Malamin ya ce gwamnatin da kanta, ta bakin kwamishinan ilimi na jihar, ta tabbatar da cewa abinda ake yi masa zalunci ne amma ta dakatar da shi ba tare da bashi damar ya kare kansa ba.

Abdul-jabbar ya yi wannan jawabin ne biyo bayan rufe masallacinsa da ke makarantarsa da gwamnatin Kano ta yi a ranar Laraba gami da hana saka karuntunsa a gidajen rediyo da kafafen sada zumunta na jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel