'Yan bindiga sun aika mutum 2 lahira, jami'an tsaro sun ceto mutum 19 a Kaduna

'Yan bindiga sun aika mutum 2 lahira, jami'an tsaro sun ceto mutum 19 a Kaduna

- Mutum biyu sun rasa ransu sakamakon musayar wuta da aka yi tsakanin 'yan bindiga da 'yan sa kai

- 'Yan bindiga sun shiga karamar hukumar Zaria inda suka kwashe mutum biyar daga gida daya

- Jami'an tsaro sun yi nasarar ceto wasu mutane 14 da wasu 5 da aka yi garkuwa da su a Birnin Gwari

Rayuka biyu aka rasa yayin da wasu 'yan bindiga suka kai hari karamar hukumar Zaria da ke jihar Kaduna, Channels Tv ta wallafa.

'Yan bindigan sun kara da sace babura hudu daga karamar hukumar yayin da suke aika-aikar.

Kamar yadda takardar da kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya fitar, 'yan bindigan sun kutsa kauyen inda suka kai hari gidan wani Abdulazeez Sani.

Sun sace matarsa mai suna Samira Abdulazeez tare 'ya'yansa biyu, Aliyu da Lawal Abdulazeez tare da wata mata Halima M. Sani da dan ta.

'Yan bindiga sun aika mutum 2 lahira, jami'an tsaro sun ceto mutum 19 a Kaduna
'Yan bindiga sun aika mutum 2 lahira, jami'an tsaro sun ceto mutum 19 a Kaduna. Hoto daga @Vanguardngrnews
Source: Twitter

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun bindige miji, mata da diyarsu a cikin wata coci a Anambra

A yayin da 'yan bindigan suka yi awon gaba da wadanda suka sace, 'yan sa kai da ke kauyen Ungwan mai Turmi a karamar hukumar Igabi sun tare su.

Musayar wutar da aka yi ce ta sa 'yan bindigan suka saki wadanda suka sato domin ceton kansu.

'Yan bindigan sun tsere inda suka ratsa ta kauyen Ungwan Hazo da ke Zaria tare da kashe wasu mutum biyu da kuma raunata wasu

A wani cigaba na daban, an sace wasu mutum 14 amma an ceto su a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

Jami'an tsaro sun ceto wasu mutum biyar a Unguwan Maka da ke Dutsen Abba a karamar hukumar Zaria.

KU KARANTA: El-Rufai ya kushe yadda ake fatattakar 'yan Najeriya daga wasu sassan kasar nan

A wani labari na daban, kungiyar gwamnonin arewa (NEF) ta yi kira a kan a daina harar Fulani makiyaya da ke kudu maso gabas, kudu maso yamma da kuma kudu-kudu a kasar nan.

Gwamnonin sun ce akwai bukatar a kiyayi makiyaya da babu ruwansu sannan a mika masu laifi hannun hukumomin tsaro.

Amma gwamnonin kudu maso yamma sun yi martani ga wannan kiran inda suka ce akwai bukatar hukumomi a arewacin Najeriya su dakatar da makasan makiyaya da ke zabga barna a kudu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel