Duniya da faɗi take: Mijin Zahra Buhari ya caccaki matar da ta tsokanesa kan riga-kafin COVID-19

Duniya da faɗi take: Mijin Zahra Buhari ya caccaki matar da ta tsokanesa kan riga-kafin COVID-19

- Mijin Zahra Buhari ya wallafa hotonsa kwanan nan inda yake karbar allurar rigakafi a wajen kasar

- Wata matashiyar budurwa ta tambaye shi game da wadanda za su karbi wanda Shugaba Buhari ke son siyowa

- Mijin Zahra ya fada wa matashiyar cewa yana da yancin karbar rigakafin a duk inda yake so

Mijin Zahra Buhari, Ahmed Indimi ya yi martani ga wata budurwa da ta yi masa ba’a a kan yin allurar rigakafin korona a wajen kasar.

Lamarin ya fara ne lokacin da Ahmed ya je shafinsa na Instagram don wallafa hotonsa yayinda yake karbar rigakafin.

KU KARANTA KUMA: Saurayi ya maka budurwa kotu bayan tura mata N5K amma taƙi zuwa ɗakinsa

Kowa na da yancin yin abunda ya so: Mijin Zahra Buhari ya mayar da martani ga budurwar da ta caccake shi kan yin rigakafin korona a kasar waje
Kowa na da yancin yin abunda ya so: Mijin Zahra Buhari ya mayar da martani ga budurwar da ta caccake shi kan yin rigakafin korona a kasar waje Hoto: @ahmed.indimi
Asali: Instagram

Sai wata matashiya a shafin mai suna originalkitchenfamacy tayi martani ga hoton a sashinsa na yin sharhi.

Matar ta bayyana cewa Ahmed da sauran masu kudi suna uduwa kasar waje don yin rigakafin. Har tayi tambaya game da wadanda za su karbi wadanda shugaba Buhari wanda ya kasance surukinsa zai siya wa yan Najeriya.

Da yake martani ga budurwar, mijin Zahra ya fada mata cewa ta kwantar da hankalinta. Da ya ke cewa ba zai sauke wallafar da yayi ba saboda shafinsa ne, Ahmed ya bayyana cewa yana da yancin yin rigakafin a duk inda ya so.

A cewarsa, baya rike da kowani mukamin gwamnati.

KU KARANTA KUMA: Hukumar yan sanda ta sanar da kyautar N10m ga duk mutumin da ya iya bayyana inda wasu masu laifi suke

Ahmed ya bayyana cewa dalilinsa na wallafa hoton don kawai ya karfafa wa mutane gwiwar yin rigakafin ne domin yana da inganci kuma yana iya ceton rayuwarsu.

Karanta hirar tasu a kasa:

Kowa na da yancin yin abunda ya so: Mijin Zahra Buhari ya mayar da martani ga budurwar da ta caccake shi kan yin rigakafin korona a kasar waje
Kowa na da yancin yin abunda ya so: Mijin Zahra Buhari ya mayar da martani ga budurwar da ta caccake shi kan yin rigakafin korona a kasar waje Hoto: @ahmed.indimi
Asali: Instagram

A baya mun ji cewa Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa allurar rigafin COVID-19 ce kawai mafita don shawo kan cutar.

Harma, Shugaban kwamitin PTF, Boss Mustapha, ya bayyana cewa yan Najeriya da dama na iya mutuwa idan ba rigakafin.

Mustapha ya kuma bayyana cewa kasashe a fadin duniya za su fara bukatar shaidar yin rigakafin kafin su ba matafiya damar shiga cikinsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng