Gwamnatin jihar Legas za ta fatattaki masu talla a kan titunan jihar
- Gwamnatin jihar Legas ta yi kudurin fatattakar dukkan masu talla a kan titunan jihar
- Wannan wani yunkuri ne na samar da ingantaccen tsafta da kiyaye lafiyar 'yan jihar
- Gwamnatin jihar ta koka kan yadda masu tallan ke bata cikin birnin da shara haka siddan
Gwamnatin Jihar Legas ta nuna matukar damuwa game da yadda ake zubar da shara ba bisa ka’ida ba da kuma karuwar adadin masu yin talla a manyan titunan mota, Daily Trust ta ruwaito.
A dalilin haka, ta umarci hukumar tsabtace muhalli ta jihar (LAGESC) da ta kori 'yan tallan da ke yawo a kan manyan hanyoyin jihar.
Kwamishinan Muhalli da Albarkatun Ruwa, Mista Tunji Bello, ya bayyana hakan yayin ziyarar aiki da ya kai LAGESC.
Mista Bello ya ce, "Akwai bukatar jami'an LAGESC su tabbatar da cewa duk manyan hanyoyi a cikin jihar sun kubuta daga duk wata matsala ta muhalli da keta doka domin tabbatar da tsaftar muhalli gaba daya."
KU KARANTA: Buhari ya amince da bai wa sabbin jami’o’i 20 masu zaman kansu lasisi
Bello ya lura da karuwar masu talla a wasu manyan tituna a tsibirin Victoria da kuma Mainland, inda ya umurci jami’an LAGESC da su shige gaba don tabbatar da cikakken tsafta.
A cewarsa, hanyoyin ba an yi su don cinikayya bane, kuma ya kamata mutane su shiga kasuwannin da jihar ta amince da su don gudanar da ayyukan kasuwanci na doka.
Sannan ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da ba da taimako da goyon baya da suka dace kamar karfafa ma'aikata, inshora da ingantaccen aiki yadda ya kamata.
Kwamishina, saboda haka, ya gargadi jami'an da su guji duk wani nau'i na ayyukan rashin tsafta, yana mai gargadin cewa duk wani jami'in da aka samu yana da laifi za a hukunta shi yadda ya dace.
Tun da farko a jawabin maraba, LAGESC Corps Marshal, CP Akinpelu Gbemisola (Rtd), ta ce ziyarar za ta “kara wa ma’aikata kwarin gwiwa kuma ta sa su ji cewa su ma suna da mahimmanci wajen ci gaban wannan gwamnati.”
KU KARANTA: Cikin Hotuna: Sheikh Abubakar Gumi ya gana da shugabannin 'yan bindiga a Zamfara
A wani labarin, Wasu yara 2, Maryam Abubakar da Abdulkadir Abubakar sun rasa rayukansu bayan sun sha wani tsumi da mai maganin gargajiya ya basu.
Mahaifiyarsu, Sadiya Abubakar, yanzu haka bata san inda kanta yake ba, likitoci suna iyakar kokarin ganin sun ceto rayuwarta a asibiti.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng