Cikin Hotuna: Yan ta'addan Boko Haram sun kwace motocin yan sanda a Borno
- Yan ta'addan Boko Haram sun kai wa yan sandan Nigeria hari a Borno
- Sun kwace motoci biyu na yan sanda a yayin harin
- Hakan ya faru ne yayinda suka kai hari chek point din yan sandan
Kungiyar ta'addan Boko Haram ISWAP, masu lakani da Jamā'at Ahl as-Sunnah lid-Da'wah wa'l-Jihād, sun ragargaza motoci biyu da kungiyar ta kwato daga yan sandan Nigeria.
A wani jawabi da kungiyar ta saki wanda SaharaReporters ta gani ranar laraba, sun kwaci motocin ne yayinda kungiyar ta kai hari wani chek point din yan sanda a hanyar Maiduguri-Chabal-Magumeri a jihar Borno.
Kauyen Chabal a karamar hukumar Magumeri yana da kilo mita 22 daga tashar Maimalari, 7 na marabar sojojin Nigeria a Maiduguri.
KU KARANTA: 'Mu ma abin ya ishe mu', 'Yan Bayelsa sun nemi a fattaki makiyaya daga jiharsu
A jawabin da yan ta'addan suka saki sun bayyana cewa sunyi garkuwa da yan sanda da mutane da yawa a yayin harin.
A baya mun samu labari daga SaharaReporters yadda yan ta'addan suka kashe yan sanda biyu da wani mutum a kauyen Chabal.
"Yanzu muka samu labari cewa yan ta'addan Boko Haram sun kai wa wasu yan sanda hari a kauyen Chabal. An kuma harbi wani dan sa kai. An tura Sojoji daga Maimalari zuwa wajen," wata majiya daga sojoji ta fadawa SaharaReporters ranar Lahadi.
A watannin baya, yan ta'addan sun sha san farmakar jami'an tsaro.
KU KARANTA: Gwamnatin Kano ta hana Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara wa'azi a jihar
Mutane sama da 30,000 sun mutu a sanadiyyar Yan ta'addan Boko Haram sannan sun raba miliyoyin mutane da gidajensu a jihohin Adamawa, Borrno da Yobe.
Bukatar su, suna san kalifa na musulunci a arewacin Nigeria.
Yan ta'addan sun kuma lalata wani sabon makamin yaki da suka kwato daga sojojin Nigeria wancan watan.
Sun kuma lalata wani FV103 Spartan APC duk da suka kwato a wajen sojoji.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng