Yanzu-yanzu: An tsinto rubabbiyar gawar yariman da aka yi garkuwa da shi

Yanzu-yanzu: An tsinto rubabbiyar gawar yariman da aka yi garkuwa da shi

- Wani babban jami'in tsaro ya tabbatar da yadda aka tsinci gawar wani yarima mazaunin Atlanta, Eloniyo Dennis Abuda

- Dama an yi garkuwa da yariman ne a Edo a ranar 30 ga watan Janairun 2020, sai aka tsinci gawarsa a daji

- Sai dai an nemi jin ta bakin jami'in hulda da jama'an 'yan sandan jihar Edo, SP Chidi Nwabuzor, amma ba a samu nasara ba

Bayan sace wani yarima mazaunin Atlanta a ranar 30 ga watan Janairun 2020 a jihar Edo, kwatsam yau aka tsinci rubabbiyar gawarsa a daji.

Wani babban jami'in tsaro ne ya tabbatar da tsintar gawar yariman, The Nation ta wallafa.

Sai dai har yanzu ba a samu damar ganawa da jami'in hulda da jama'an jihar ba, SP Chidi Nwabuzor.

KU KARANTA: Duk da rade-radin maye gurbinsa, IGP ya tarba shugaba Buhari bayan sauka Abuja daga Daura

Yanzu-yanzu: An samu rubabbiyar gawar yariman da aka yi garkuwa da shi
Yanzu-yanzu: An samu rubabbiyar gawar yariman da aka yi garkuwa da shi. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Aisha Yesufu ta yi wa Nnamdi Kanu wankin babban bargo a kan Fulani makiyaya

Karin bayani na nan tafe...

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng