Yara 2 sun sheka lahira, mahaifiyarsu ta jigata bayan shan maganin gargajiya a Kano

Yara 2 sun sheka lahira, mahaifiyarsu ta jigata bayan shan maganin gargajiya a Kano

- Yara biyu, Maryam Abubakar da Abdulkadir Abubakar, sun mutu bayan sun sha wani tsumi da mai maganin gargajiya ya basu

- Mahaifiyarsu, Sadiya Abubakar, tana asibiti rai a hannun Allah, likitoci suna ta kokarin ganin sun ceto rayuwarta

- Wannan lamarin ya faru ne a ranar Talata a Kwarin Barke dake Sabuwar Gandu a karamar hukumar Kumbotso dake jihar Kano

Wasu yara 2, Maryam Abubakar da Abdulkadir Abubakar sun rasa rayukansu bayan sun sha wani tsumi da mai maganin gargajiya ya basu.

Mahaifiyarsu, Sadiya Abubakar, yanzu haka bata san inda kanta yake ba, likitoci suna iyakar kokarin ganin sun ceto rayuwarta a asibiti.

Al'amarin ya faru ne a ranar Talata a Kwarin Barke dake Sabuwar Gandu a karamar hukumar Kumbotso dake jihar Kano, Daily Trust ta wallafa.

KU KARANTA: Duk da rade-radin maye gurbinsa, IGP ya tarba shugaba Buhari bayan sauka Abuja daga Daura

Yara 2 sun sheka lahira, mahaifiyarsu ta jigata bayan shan maganin gargajiya a Kano
Yara 2 sun sheka lahira, mahaifiyarsu ta jigata bayan shan maganin gargajiya a Kano. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

Kakakin hukumar 'yan sandan jihar, DSP Abdullahi Kiyawa ya ce bayan 'yan sanda sun yi bincike ne suka ga wata gora cike da wani maganin gargajiya da wata gorar koko a gefen gawawwakin a dakin da aka same su.

A cewarsa, maganin gargajiyan da suka sha ne yayi ajalinsu kuma ya sanya mahaifiyarsu a mawuyacin hali.

Ya kara da cewa an kai gawawwakin asibiti don binciko asalin silar mutuwarsu.

KU KARANTA: Aisha Yesufu ta yi wa Nnamdi Kanu wankin babban bargo a kan Fulani makiyaya

A wani labari na daban, wani Charles Majawa ya sheka lahira sakamakon tsananin gamsuwar da yayi yayin da yake saduwa da wata mata.

Rahoton 'yan sanda ya bayyana cewa matashin mai shekaru 35 ya suma bayan saduwa da matar a yankin Phalombe da ke Malawi.

Ya mutu jim kadan bayan kammala lalatar kuma bincike da likitoci suka yi ya nuna cewa tsabar gamsuwa da dadi ne suka sa ya rasu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng