Hoton dankareriyar motar miliyoyin naira da Emmanuella ta siya ya janyo cece-kuce

Hoton dankareriyar motar miliyoyin naira da Emmanuella ta siya ya janyo cece-kuce

- Yarinya mai wasan barkwanci, Emmanuella, ta wallafa wasu hotuna da suka gigita jama'a

- An ga Emmanuella tare da wata kawarta sun karkace a gefen motarta kirar Lexus 570

- Yarinyar mai wasan barkwanci ta janyo maganganu kala-kala daga masoyanta

Yarinya mai wasan barkwaci, Emmanuella ta janyo cece-kuce a kafar sada zumuntar zamani bayan ta wallafa wasu hotuna a shafinta na Instagram.

A hotunan, an ga yarinyar tare da wata kawarta suna tsaye bayan wata hadaddiyar mota suna yi wa masoyanta fatan alheri.

Hotunan sun bayyana wata mota kirar Lexus 570 mai darajar miliyoyin naira.

KU KARANTA: Kotun Abuja ta bada umarnin garkame kasuwar Wuse saboda take dokar korona

Hoton dankareriyar motar miliyoyin naira da Emmanuella ta siya ya janyo cece-kuce
Hoton dankareriyar motar miliyoyin naira da Emmanuella ta siya ya janyo cece-kuce. Hoto daga Officialemmanuella
Asali: Instagram

KU KARANTA: Kotun Abuja ta bada umarnin garkame kasuwar Wuse saboda take dokar korona

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, Emmanuella bata dade da siyan dankareriyar motar ba.

Wannan wallafar ta janyo maganganu inda masoyanta da mabiyanta suka dinga mata Allah sam barka tare da taya ta murna.

Ga wasu daga cikin tsokacin:

yes_i_am_uche cewa yayi: "Wannan ba abun wasa bane, ina taya ki murna yarinya."

temmyl ta yi tsokaci da: "Ku taya ta murna ku kara gaba, babu tsokaci mara dadi ya ku jama'an duniya!"

teeto_olayeni ta ce: "Ina taya ki murna."

A wani labari na daban, fitacciyar 'yar gwagwarmayar nan, Aisha Yesufu sun yi cacar baki da Nnamdi Kanu a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter.

A ranar Lahadi, 31 ga watan Janairu Nnamdi Kanu ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na Facebook inda yake nuna jami'an tsaron kudu, ESN, suna hantarar Fulani a sansaninsu dake Isuikwuato, jihar Abia, inda suka yi ta fatattakarsu suna kashe musu shanu.

Wannan bidiyon ya fusata Yesufu, inda ta caccaki lamarin har take cewa hakan bai dace ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel