Ba mu da ikon dakatar da yajin-aikin ranar Juma’a inji wakilan SSANU da NASU
- Gwamnatin Tarayya ta yi zama da kungiyoyin Ma’aikatan Jami’a a Abuja
- Kungiyoyin NASU da SSANU sun ce suna nan a kan batun tafiya yajin-aiki
- Wakilan kungiyoyin za su zauna da ‘ya ‘yansu kafin su dauki wata matsaya
A ranar Talata, 2 ga watan Fubrairu, 202 ne kwamitin hadaka na kungiyoyin SSAN da NASU su ka tabbatar da cewa maganar yajin-aikin su ta na nan.
Shugaban kungiyar SSANU, Mohammed Haruna Ibrahim da sakataren NASU na kasa, Peters Adeyemi, su ka bayyana wa ‘yan jarida wannan a Abuja.
Jawabin na Malam Mohammed Haruna Ibrahim da Mista Peters Adeyemi ya zo ne bayan sun shafe tsawon sa’o’i uku su na tattaunawa da gwamnati.
Da yake yi wa ‘yan jarida jawabi bayan taron, Peters Adeyemi, ya ce a matsayinsu na shugabannin kungiya, ba su da ikon su hana ‘ya ‘yansu tafiya yajin-aiki.
KU KARANTA: Ma'aikatan Jami'o'i za su fara sabon yajin aiki a watan nan
Sakataren na NASU ya ce: “Ba mu da hurumin da za mu yi magana a kan dakatar da yajin-aiki, ya fi karfinmu. Har gobe wannan ne matsayar ‘ya ‘yanmu.”
“Maganarmu ta na nan, har sai an ce mu dakata. Ba mu kammala maganar ba. Akwai sauran abubuwa da su ka taso wajen tattaunawarmu.” Inji Adeyemi.
Yace za su koma zuwa wajen ‘ya ‘yan kungiyar su fada masu yadda aka yi, daga nan sais u yanke hukuncin ko a shiga yajin-aiki, ko kuma a dakata da maganar.
Gwamnatin tarayya ta ba wakilan ‘yan kwadagon lokaci su je ta gana da ‘ya ‘yan kungiyar kafin su dauki wani mataki, amma ana sa ran cewa a shawo kan su.
KU KARANTA: IPPIS: SSANU, NASU suna zanga-zanga a Najeriya
A jiya kun ji gwamnati za ta yi zama da ma’aikatan jami’a a kan sabon yajin-aiki. Chris Ngige ya ce zai sa labule da ma’aikatan a karkashin SSANU da NASU.
Idan za ku tuna, Ministan kwadago, Sanata Chris Ngige ne ke jagorantar wannan zaman da ake yi.
Kungiyoyin ma’aikatan za su tafi yajin-aiki na din-din-din ne domin nuna rashin goyon bayansu game da yadda ake rabon alawus din da aka ba jami’io’i.
An samu sabani ne tsakanin ma’aikatan jami’o’in a sakamakon alawus da gwamnatin tarayya ta fitar, kungiyoyin SSANU da NASU ke ganin an kware su.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng