COVID-19: PTF ta ce Kogi jiha ce mai tarin hatsari, ta ja kunnen 'yan Najeriya a kan ziyara

COVID-19: PTF ta ce Kogi jiha ce mai tarin hatsari, ta ja kunnen 'yan Najeriya a kan ziyara

- Kwamitin PTF na fadar shugaban kasa ya bayyana jihar Kogi a matsayin dandalin cutar korona

- Kwamitin ya ce jihar bata yadda da wanzuwar cutar korona ba balle ta dinga gwaji ko killace masu ita

- Dr Mukhtar Muhammad ya ja kunnen 'yan Najeriya da su kauracewa kai ziyara jihar domin tseratar da kansu

Kwamitin fadar shugaban na yaki da cutar korona (PTF) ta bayyana jihar Kogi a matsayin jihar da ta fi kowacce hatsari a fannin yaduwar cutar korona. Ta ce jihar bata yadda da wanzuwar cutar ba kwata-kwata.

Kwamitin PTF ya ce gwamnatin Kogi ta kasa bada rahoton gwaji, bata da cibiyar killacewa kuma hakan ta sa ake jan kunnen 'yan Najeriya da su kiyayi ziyartar jihar.

Kwamitin ya ce ya binciko tare da bankado wasu kananan hukumomi 22 a cikin jihohi 13 na kasar nan da annobar ta yi kamari, Vanguard ta wallafa.

KU KARANTA: Da duminsa: APC ta yi sasanci tsakanin Yari da Marafa a jihar Zamfara (Hotuna)

COVID-19: PTF ta ce Kogi jiha ce mai tarin hatsari, ta ja kunnen 'yan Najeriya a kan ziyara
COVID-19: PTF ta ce Kogi jiha ce mai tarin hatsari, ta ja kunnen 'yan Najeriya a kan ziyara. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

Dr Mukhtar Muhammad ya sanar da hakan a Abuja inda yace: "Bugu da kari, muna da jihohi da suka ki bada bayani. Idan ba mu yi gwaji ba, babu yadda za samu bayanai.

"Jihohin da cutar ta fi kamari suna hada da Yobe, Jigawa, Zamfara da kebbi sai kuma jihar Kogi da ke da tarin hatsari.

"Duk jihohin da ba a gwaji dole mu saka su a cikin masu tarin hatsaru kuma ana shawartar 'yan Najeriya da su kiyaye kai ziyara. Koda kun fadi ciwo babu cibiyoyin killacewa."

KU KARANTA: Dalilin da yasa Buratai da sauran tsoffin hafsoshin tsaro suka gaza, Wike ya fasa kwai

A wani labari na daban, shiru ake ji dangane da batun zaben sabon Sifeta janar na 'yan sanda sakamakon karewar wa'adin IGP Mohammed Adamu a ranar Litinin.

Fadar shugaban kasa bata sanar da wani tsayayyen lokaci ba na sanar da wanda zai gaji kujerarsa ba, The Nation ta wallafa.

Kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, a ranar Litinin da ana tattaunawa da shi a gidan talabijin din Channels ya ce bai san komai ba dangane da al'amarin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel