Matashi ya sheka lahira saboda 'tsabar gamsuwa' bayan kwana da budurwa a otal

Matashi ya sheka lahira saboda 'tsabar gamsuwa' bayan kwana da budurwa a otal

- Matashi mai shekaru 35 ya sheka lahira saboda tsananin gamsuwa da dadin budurwar da ya kwana da ita

- An gano cewa, bayan kammala saduwa da budurwar, ya fita hayyacinsa daga nan ya ce ga garinku

- Budurwar ta kira 'yan sanda wadanda suka kwashe shi sai asibiti kuma aka tabbatar da dalilin mutuwar

Wani Charles Majawa ya sheka lahira sakamakon tsananin gamsuwar da yayi yayin da yake saduwa da wata mata.

Rahoton 'yan sanda ya bayyana cewa matashin mai shekaru 35 ya suma bayan saduwa da matar a yankin Phalombe da ke Malawi.

Ya mutu jim kadan bayan kammala lalatar kuma bincike da likitoci suka yi ya nuna cewa tsabar gamsuwa da dadi ne suka sa ya rasu.

KU KARANTA: Alkali ya bayyana boyayyen sirrin da aka gano a kan 'ya'yansa uku bayan gwajin DNA

Matashi ya sheka lahira saboda 'tsabar gamsuwa' bayan kwana da budurwa a otal
Matashi ya sheka lahira saboda 'tsabar gamsuwa' bayan kwana da budurwa a otal. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

Kamar yadda Daily Star ta wallafa, matar ta yanke hukuncin kai wa 'yan sanda rahoto tare da wata abokiyar aikinta.

Bayan nan ne aka dauka gawarsa aka mika asibiti inda aka tabbatar da dalilin mutuwarsa, The Nation ta wallafa.

'Yan sandan sun tabbatar da cewa ba za a kama matar a kan mutuwar matashin ba saboda babu laifin da ta aikata.

An dauka gawar Majawa inda aka mika ta kauyensu na Matepwe.

KU KARANTA: Kotun Abuja ta bada umarnin garkame kasuwar Wuse saboda take dokar korona

A wani labari na daban, Anthony Ezonfade Okorodas wani alkali ne a jihar Delta wanda ya bada labarin yadda gwajin DNA ya bankado cewa ba shi ne mahaifin 'ya'yansa uku ba da tsohuwar matarsa.

A wata takarda da ya bai wa manema labarai a ranar 28 ga watan Janairu, Okorodas ya ce ya yanke hukuncin fallasa sirrin ne domin gujewa maganganun jama'a da kuma karya da za a yi a kansa.

Alkalin ya zargi Celia Juliet Ototo, tsohuwar matarsa da barin aurensu na shekaru 11 a lokacin da autansu yake da shekaru shida a duniya, The Cable ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel