Fasto Tunde Bakare ya yi kakkausar suka a kan gwamnatin Buhari

Fasto Tunde Bakare ya yi kakkausar suka a kan gwamnatin Buhari

- Fasto Tunde Bakare ya caccaki gwamnatin shugaba Buhari

- Ya zarge ta da mayar da Najeriya baya

- Ya zuwa yanzu gwamnati bata mayar da martani ba

Abokin takarar shugaba Buhari a zaben shekarar 2011 karkashin tsohuwar jam'iyyar APC, Fasto Tunde Bakare, ya caccaki gwamnatin shugaba Buhari, ya ce gwamnatin ta jawo wa Najeriya koma-baya.

Mista Bakare ya bayyana haka ne yayin wa'azin ranar Lahadi a cocinsa dake jihar Legas.

Fasto Tunde Bakare ya yi kakkausar suka a kan gwamnatin Buhari
Fasto Tunde Bakare

"Wannan gwamnatin ta samu nasarar cin zabe ne ta hanyar yi wa 'yan Najeriya alkawura guda uku da suka hada da; yaki da cin hanci da rashawa, tabbatar da zaman lafiya, da samar da aiki ga matasa kuma ta gaza a dukkan alkawuran da ta dauka," a cewar Tunde Bakare.

DUBA WANNAN: Ka canja salon mulkin ka tun kafin jama'a su canja ka - Fasto Mbaka ya fadawa Buhari

"Adadin marasa aikin yi ya karu daga mutum miliyan 6 zuwa 16 daga hawan gwamnatin. Ko a yaki da cin hancin ma bata yi wata nasara ba. Misali, sau hudu gwamnatin na shan kaye a kotu cikin sa'o'i 96 a kan tuhume-tuhumen yaki da cin hanci," Tunde Bakare ya fada.

Kazalika, Faston, ya zargi gwamnatin da gazawa ta fuskar tsaro, yana mai bayar da misali ga kashe-kashe da yawaitar hare-hare da suka kunno kai tun shigowar shekarar nan.

Fasto Bakare ya zargi gwamnatin shugaba Buhari da rashin daukan matakan kiyaye afkuwar tashe-tashen hankula da Najeriya ke fama da su.

Ya zuwa yanzu dai gwamnatin bata mayar wa da Fasto Bakare raddi ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel