An rasa rayuka 5, gidaje da shaguna sun babbake bayan kutse 'yan bindiga a Sokoto

An rasa rayuka 5, gidaje da shaguna sun babbake bayan kutse 'yan bindiga a Sokoto

- 'Yan sandan jihar Sokoto sun bayyana yadda wasu 'yan bindiga suka kashe mutane 5 a kauyen Adamawa dake karamar hukumar Sabon Birni dake jihar

- Kamar yadda jami'in hulda da jama'ar 'yan sandan, ASP Abubakar Sadiq ya tabbatar da yadda daruruwan 'yan bindigan suka kai hari kauyen

- Sai da suka kona shaguna 6, gidaje 11 sannan suka kashe mutane 5, sun kuma harbi mutane da dama sannan suka afka wa wasu kauyakun daban

'Yan sandan jihar Sokoto sun bayyana yadda wasu 'yan bindiga suka kashe mutane 5 a kauyen Adamawa dake karamar hukumar Sabon Birni dake jihar, The Punch ta ruwaito.

Jami'in hulda da jama'a, ASP Abubakar Sadiq ne ya tabbatar da yadda daruruwan 'yan bindigan suka afka kauyen Adamawa a baburansu, inda suka kona shaguna 6, gidaje 11, sannan suka harbi wasu mutane 5 duk 'yan kauyen.

KU KARANTA: Kotun Abuja ta bada umarnin garkame kasuwar Wuse saboda take dokar korona

An rasa rayuka 5, gidaje da shaguna sun babbake bayan kutse 'yan bindiga a Sokoto
An rasa rayuka 5, gidaje da shaguna sun babbake bayan kutse 'yan bindiga a Sokoto. Hoto daga @MobilePunch
Asali: UGC

A cewarsa, "Sannan 'yan bindigan sun nufi kauyen Samaye inda suka sace dabbobi da sauran kayan amfanin 'yan kauyen."

ASP Sadiq ya kara bayyana yadda al'amarin ya faru da misalin karfe 12:00am na ranar 12 ga watan Janairu, kuma suka cigaba da barna na tsawon sa'o'i biyu.

A cewarsa, 'yan sandan sun lallaba har kauyen amma basu samu nasarar kama kowa ba.

KU KARANTA: Alkali ya bayyana boyayyen sirrin da aka gano a kan 'ya'yansa uku bayan gwajin DNA

A wani labari na daban, kwamitin fadar shugaban na yaki da cutar korona (PTF) ta bayyana jihar Kogi a matsayin jihar da ta fi kowacce hatsari a fannin yaduwar cutar korona. Ta ce jihar bata yadda da wanzuwar cutar ba kwata-kwata.

Kwamitin PTF ya ce gwamnatin Kogi ta kasa bada rahoton gwaji, bata da cibiyar killacewa kuma hakan ta sa ake jan kunnen 'yan Najeriya da su kiyayi ziyartar jihar.

Kwamitin ya ce ya binciko tare da bankado wasu kananan hukumomi 22 a cikin jihohi 13 na kasar nan da annobar ta yi kamari, Vanguard ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: