Tsofaffin kwanonin nan ba za su mika maku mulki ba – Obasanjo ya zugo Matasa
- Olusegun Obasanjo ya yi magana a kan matasa da harkar shugabancin Najeriya
- Tsohon shugaban ya ce matasan da ke tasowa ba za su tsinci mulki da araha ba
- Obasanjo ya ba matasa hakuri, ya yi kira gare su da su tashi su nemi shugabanci
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya kulabalanci matasan Najeriya da su kawo canji a Najeriya ta hanyar canza wanda zai rike shugabanci.
Da yake jawabi a wata hira da aka yi da shi a ranar Asabar, Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa sa’o’insa sun aikata ba daidai ba iri-iri a Najeriya.
Kamar yadda jaridar Punch ta fitar da rahoto, an yi hira da tsohon shugaban kasar ne ta kafar yanar gizo, inda har ya ba matasa hakurin ta’asar da aka yi.
Olusegun Obasanjo ya yi kira ga matasan kasar da su yi abin da za su iya domin su hana dattawan da ya kira ‘tsofaffin kwanoni’ sakat a kujerun mulki.
KU KARANTA: Ya kamata Shugaban kasa ya fito daga Kudu - Gaya
Dattijon ya fada wa matasan cewa ka da su tsaya su na koka wa, domin su ne shugabannin gobe.
Obasanjo wanda ya yi mulkin farar hula tsakanin 1999 da 2007 ya ce tsofaffin da ke rike da madafan iko, ba za su bada mulki ta dadi ba, sai ‘an fatattake su.’
Ya ce: “Ku daina zama haka nan ku na kokawa. Zama ku na kuka ba zai kai ku ko ina ba, dole ku samu hadin-kan tulin mutane irinku da za su kawo sauyi.”
Obasanjo ya kara da cewa: “Idan mutane su ka ce yaushe tsofaffin nan za su tafi? Ina fada masu cewa ba za su tafi ba, sai dai ku yi abin da zai sa su bada wuri.”
KU KARANTA: Majalisa ta yi magana a kan hana Makiyaya tashi daga Arewa zuwa Kudu
“Haka nan ba za su bada mulki da kansu ba, sai dai idan kun hana su sake wa.” Inji Obasanjo.
Adamu Garba wani matashin da ya nemi ya yi takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar APC a 2019 ya fadi yankin da zai sha wuya idan Najeriya ta barke.
Wannan matashi ya ce idan aka duba sarai, ko gobe aka barka kasar nan, yankin Arewa ba zai tagayyara ba domin Ubangiji ya yi wa kasar tarin arziki mai yawa.
A cewarsa, ba Arewa ba, sauran bangarori ne za su sha wahala idan da za a raba Najeriya.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng