"Ba Arewa ba, sauran bangarori ne za su sha wahala idan da za a raba Najeriya"
Tsohon mai neman takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC, Mista Adamu Garba, ya yi ikirarin cewa yankin Arewa ya fi kowane arziki a kasar nan.
Matashin ‘dan siyasar ya nuna cewa Arewa ta na da duk arzikin da ake bukata wanda za ta dogara da shi ko da kuwa an yi nasarar raba Najeriya wata rana.
A cewar Adamu Garba, sauran bangarori ne za su sha wahala idan har aka ce Najeriya ta barke.
Ga wasu dalilai da ya kawo kamar yadda ya yi bayani a shafinsa na Twitter:
1. Arewa ce ta ke da mafi yawan kayan arzikin da ake amfani da su a duk kamfanonin Najeriya, daga na gona, tufafi, zuwa kayan gini.
2. Arewa ta na da gwal, kanwa, gawayi, karfe, magnesium, har da ‘uranium’ da sauransu.
3. Arewa ta na da kogin Neja wanda ya taho tun daga tsaunakun Guinea, ya ratsa Kebbi, Neja, Kogi zuwa Delta inda ake kira Neja-Delta. Arewa ta yi iyaka da Benin zuwa kogin Maliya ta kasar Borgu.
KU KARANTA:
Garba ya cigaba da kawo dalilansa:
4. Za a samu kasuwanci tsakanin Najeriya da Kotono saboda ‘Yan Arewa da su ka yi karatu a jami’o’in Benin.
5. Arewa za ta iya yashe kogin Neja ta Benin, ta hadu da kogin Maliya ko a samu datse ta kasar Nijar zuwa Guinea.
6. Idan aka toshe Kogin Neja daga Arewa, ruwa zai tsaya a rafukan Imo, Onistsha da na yankin Delta, duka halittun ruwan da ke nan za su mutu.
7. Arewa ta ke da manyan jeji, daga dajin Borgu zuwa Felgore, Yankari, Gashaka har Sambisa.
8. Arewa ke da kogin Benuwai, wanda ya shiga duka jihohin Arewa maso gabas ta tsakiya. Wannan kogi ya hada Najeriya da Kamaru, Chad, Benin, da Nijar a Afrika.
KU KARANTA:
9. Arewa ta ke da eka miliyan 71 cikin eka miliyan 78 na kasar noma da ake da shi a Najeriya. Za a samu hatsi da kayan gona daga yankin.
10. Arewa ta na da abokai a gabas ta tsakiya da Israila, da kuma kasashen Turai da Amurka, da irinsu kasashen Rasha da Sin.
11. Yankin Arewa na da hanyar samun wuta daga ruwa, iska, gas, har zuwa nukiliya.
12. Arewa ta na da tsarin karatu, kiwon lafiya, siyasar Duniya, da tsare-tsaren harkokin kasar waje da sauransu.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng