Za mu tattauna batun hana Makiyaya yawo da dabbobi a Majalisar Wakilai Inji Kalu

Za mu tattauna batun hana Makiyaya yawo da dabbobi a Majalisar Wakilai Inji Kalu

- Majalisar Tarayya ta tabo batun hana Makiyaya kiwo zuwa Kudancin Najeriya

- Abdullahi Ganduje ya na goyon bayan a haramtawa Makiyaya yawo da dabbobi

- ‘Yan Majalisa sun ce za su duba yiwuwar a kawo kudirin domin ya zama doka

Majalisar wakilan tarayya ta ce za ta duba maganar da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kawo na kawo dokar da za ta hana makiyaya yawo.

Mai magana da yawun bakin majalisar kasar, Honarabul Benjamin Kalu ya bayyana haka a lokacin da ya yi hira da jaridar Vanguard a ranar Litinin.

Benjamin Kalu ya ce akwai bukatar majalisa ta duba wannan batu a ma’unin halin zamantake wa, siyasa da tattalin arzikin da kasar ta ke ciki a yanzu.

Da yake bayani, Hon. Benjamin Kalu ya ce majalisa za ta yi la’akari da dokokin kasar da ake da su da amfani ko akasin a ce an haramtawa makiyayan yawo.

KU KARANTA: Makiyaya iri 3 ake da su a Najeriya - Abdullahi Umar Ganduje

Kalu ya yi maganar yiwuwar kawo maganar gwamnan a matsayin kudirin da za a tattauna a zauren majalisa, inda an yi dace sai shawarar ta zama dokar kasa.

Idan an daura shawarar gwamnan na Kano a kan wannan ma’auni ne, majalisar tarayya za ta yanke hukunci ko za ta dauki shawarar, ko kuma ta yi fatali da ita.

Mai magana da yawun bakin ‘yan majalisar ya ce aikinsu shi ne su duba shawarwarin jama’a a ma’unar tsarin mulki da dokar kasa domin a samar da mafita.

A cewar Kalu, babu wani ‘dan majalisa tilo da ya isa ya zartar da hukunci a game da shawarwarin da wasu ke kawo wa, ya ce za a tattana batun ne a zauren majalisa.

Za mu tattauna batun hana Makiyaya yawo da dabbobi a Majalisar Wakilai Inji Kalu
'Yan Majalisar Wakilai Hoto: @HouseNgr
Asali: Twitter

KU KARANTA: Shugabannin Kudu sun goyi bayan Ganduje a kan matsalar makiyaya

“Na mu shi ne mu duba maganar, ba wai mu na adawa ba ne ga majalisar dattawa. Aikin mu shi ne mu daura batun a kan mizanin tsarin mulki.” Inji Hon. Ben Kalu.

Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya na ganin bai dace makiyaya su rika tashi daga yankin Arewacin Najeriya zuwa Kudancin kasar dauke da dabbobinsu ba.

Da ya ke jawabi kwanan nan a garin Daura, Abdullahi Ganduje ya bukaci a kawo wata dokar da za ta haramta yawon shanu daga arewa zuwa kudancin kasar nan.

“Ina kira a kan a yi watsi da kaiwa da kawowa ko kuma yawon makiyaya daga sassan arewa zuwa tsakiyar kasar nan ko kudancin Najeriya." inji gwamnan Kano.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng