Dalilin da yasa na ke son zama magajin Buhari a 2023, inji Fitaccen masanin kimiyar magunguna

Dalilin da yasa na ke son zama magajin Buhari a 2023, inji Fitaccen masanin kimiyar magunguna

- Fitaccen masanin kimiyyar magunguna, Mista Sam Ohuabunwa, ya ce zai fito takarar shugaban kasa a 2023

- Ohuabunwa, wanda shine shugaban kungiyar masana kimiyyar magunguna ta Nigeria, PSN ya sanar da hakan ne a wata hira da aka yi da shi a talabijin

- Ya ce ba suna ya fito nema ba kawai lokaci ne ya yi da Nigeria ke bukatar sauyi na gari kuma ya gaji da bada shawara don haka zai shiga a dama da shi

Wani fitaccen masanin kimiyyar magunguna kuma tsohon shugaban kwamitin kungiyar tattalin arziki na Nigeria, Sam Ohuabunwa ya sanar da niyyarsa na fitowa takarar shugaban kasa a 2023.

Shine shugaban kungiyar masana kimiyyar magunguna ta Nigeria, Pharmaceutical Society of Nigeria, PSN.

Dalilin da yasa na ke son zama magajin Buhari a 2023, inji Fitaccen masanin kimiyar magunguna
Dalilin da yasa na ke son zama magajin Buhari a 2023, inji Fitaccen masanin kimiyar magunguna. Hoto: Premium Times
Source: Twitter

"A shekaru na, ba wai zan fito domin wasa bane. Ba suna nake son yi ba ... Takarar da gaske zan yi," A cewar Mista Ohuabunwa mai shekaru 70 yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na TV360 Nigeria.

DUBA WANNAN: An hana wasu mata musulmai masu hijabi yin rajistan katin dan kasa, kungiyoyi sun koka

An wallafa hirar da suka yi ne a ranar Lahadi.

Mista Ohuabunwa kwararre ne da ba a san shi da shiga harkokin siyasa a Nigeria ba a baya.

Ya shaidawa wanda ke masa tambayoyin, Deji Badmus, cewa lokaci ya yi da zai shiga siyasa ya bada irin jagorancin da zai sauya kasar a maimakon ya tsaya daga baya yana bada shawarwari.

KU KARANTA: Yanzu yanzu: 'Yan PDP sun yi arangama da jami'an tsaro a Ebonyi

Mista Ohuabunwa ya ce ya dade yana kaucewa siyasa amma a Nigeria abubuwa har yanzu cigaba da tabarbarewa suke yi.

Ya ce yan Nigeria sun dade suna karbar kudade hannun yan siyasa kuma a halin yanzu sun gane cewa hakan ba zai haifar musu da da mai ido ba.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel