Matsalar makiyaya: Shugabannin Kudu sun goyi bayan Ganduje

Matsalar makiyaya: Shugabannin Kudu sun goyi bayan Ganduje

Shugabannin yankin Kudu da na tsakiyar Najeriya sun goyi bayan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano a kan kiran da yayi ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kawo dokar hana makiyaya yawo a fadin kasar nan.

Kungiyar ta SMBLF tace kiran da gwamnan yayi na da matukar amfani ga shugabannin kudu da na tsakiya.

A wata takarda da kungiyar ta saki da sa hannun Yinka Odumakin (Kudu maso yamma), Guy Ikokwu (kudu maso gabas), Sanata Bassey Henshaw da Dr Isuwa Dogo sun ce, gwamnan dan asalin kabilar makiyayan na bayyana gaskiya ne amma mai daci.

Matsalar makiyaya: Shugabannin Kudu sun goyi bayan Ganduje
Matsalar makiyaya: Shugabannin Kudu sun goyi bayan Ganduje Hoto: The Cable
Asali: UGC

Sun ce"Wannan yawace-yawacen na makiyayan na kawo hargitsi da rashin rayuka."

Kamar yadda kungiyar ta sanar, gwamnan ya jaddada cewa, "ana iya gane cewa wannan yawace-yawacen makiyayan na kawo sauki wurin safarar makamai kuma su ke kawo fadace-fadace a yankin arewa da kasar baki daya.”

KU KARANTA KUMA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Kamar yadda SMBLF tace, a wannan matsayar , gwamnan na gujewa ci gaba da rasa rayuka a fadin kasar nan.

Yana bukatar gwamnatin ta juya tare da daukar mataki a kan halin da kasar nan ke ciki.

A wani labari na daban, mun ji cewa sakamakon ci gaban fadan kabilanci tsakanin kabilar Adara da Fulani a yankin karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna, Daily Trust ta gano cewa an kashe matasa 4 'yan kabilar Adara a ranar Asabar.

'Yan uwansu ne suka konesu a kauyukan Doka sa Kallah da ke karamar hukumar Kajurun sakamakon zarginsu da suka yi da kaiwa Fulani bayanai a kansu.

An gano cewa, an banka wa Danladi Shekarau da David Kampani wuta a kauyen Doka bayan an zargesu da yin fuska biyu yayin da aka kashe Jumare Anthony a kauyen Kallah duk a kan zargi daya.

Majiya daga Doka ta tabbatar da cewa hankali ya matukar tashi a yankin. An gano su ne sakamakon kama daya daga cikin mamatan da aka yi yana tallafa wa Fulani bankawa wasu sassan kauyen wuta bayan sun kai hari a makon da ya gabata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: