Ganduje ya bukaci a haramta yawon shanu daga arewa zuwa kudancin kasar nan

Ganduje ya bukaci a haramta yawon shanu daga arewa zuwa kudancin kasar nan

- Abdullahi Ganduje, gwamnan jihar Kano ya bukaci a sanya dokar hana yawon shanu daga arewa zuwa kudu

- Ya ce za su samar da matsuguni ga makiyaya a dajin Samsosua da ke tsakanin jihar Kano da Katsina

- Ya ce hakan ne kawai zai iya sa a shawo kan matsalar rikicin manoma da makiyaya a fadin kasar na

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce ya dace a saka dokar da za ta hana kai shanu daga arewa zuwa kudu, The Cable ta wallafa.

A yayin zantawa da manema labarai bayan haduwarsa da gwamnonin APC tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Daura, jihar Katsina, Ganduje ya ce idan har ba a hana yawon shanu ba, babu ranar kawo karshen manoma da makiyaya.

Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta shirya samar da wurin zama ga makiyayan a dajin da ke tsakanin iyakar Kano da Katsina.

KU KARANTA: Dan Najeriya ya gina katafaren gida da robobin lemu da ruwa cike da kasa (Hotuna)

Ganduje ya bukaci a haramta yawon shanu daga kudu zuwa arewa
Ganduje ya bukaci a haramta yawon shanu daga kudu zuwa arewa. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Jerin sunaye: Shugabannin dakarun sojin kasa na Najeriya tun daga 1999 da jihohinsu

Ya ce matsugunin zai kasance da gidaje, tafki, cibiyar dabbobi ta zamani da asibitocin dabbobi.

"Zamu gina matsugunin a dajn Samsosua, iyakarmu da Katsina kuma mun yi nasarar shawo kan illar 'yan bindiga a yankin," Ganduje yace.

“Za mu gina gidaje, tafkuna, cibiyar dabbobi, asibitin dabbobi kuma tuni muka fara ginawa makiyayan gidaje.

“Ina kira a kan a yi watsi da kaiwa da kawowa ko kuma yawon makiyaya daga sassan arewa zuwa tsakiyar kasar nan ko kudancin Najeriya.

“A saka dokar haramcin hakan ko kuma ba za mu iya shawo kan rikici tsakanin makiyaya da manoma ba kuma ba za mu iya hana satar shanu ba da ya addabe mu."

A wani labari na daban, tsohon hafsin sojan kasa, Laftanal Janar Tukur Buratai mai murabus, ya ce ya gyara harkar sojin Najeriya fiye da yadda ya sameta.

Ya furta hakan ne a wani taron faretin saukarsa daga kujerarsa a ranar Juma'a a Abuja, Daily Trust ta wallafa.

Ya kara da cewa ya tabbatar da cewa ya bai wa sojojin cikakkiyar horarwa da kuma inganta walwalarsu.

Kamar yadda yace "Yau ranar farinciki ce ba ta takaici ba, saboda zan yi murnar barin sojojin Najeriya fiye da yadda na same su."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: