Rikicin Ekiti: Za mu kai bangaren Ayo Fayose kotun koli inji mutanen Olujimi

Rikicin Ekiti: Za mu kai bangaren Ayo Fayose kotun koli inji mutanen Olujimi

- Mutanen Biodun Olujimi za su kai bangaren Ayodele Fayose zuwa kotun koli

- Alkali ya ba su Ayo Fayose gaskiya a shari’ar zaben mazabun PDP na Ekiti

- Bangaren Sanata Olujimi sun ce sam ba za su yarda da shari’ar da aka yi ba

The Nation ta ce angaren Biodun Olujimi a jam’iyyar PDP na reshenEkiti, sun bayyana cewa za su tafi kotun koli a kan shari’arsu da mutanen Ayodele Fayose.

Mutanen Sanata Biodun Olujimi sun ce ba za su yarda da hukuncin kotun da ta tabbatar da nasarar bangaren Ayo Fayose a zaben mazabun da aka yi ba.

Wannan na zuwa ne bayan kotun daukaka kara ta yi watsi da karar da bangaren Biodun Olujimi su ka shigar, su na kalubalantar zabukan da aka yi kwanaki.

‘Yan tawaren sun fitar da jawabi ne ta bakin Sanya Adesua, wanda ya fitar da jawabi a madadin sauran ‘yan tafiyarsa bayan wani taro da su ka yi a Ado-Ekiti.

KU KARANTA: Manyan APC a Katsina sun ware, sun kafa bangare a Jam’iyya

Sanya Adesua ya ce za su kai maganar zuwa kotun koli, sannan su ka tabbatar da goyon bayansu da shugabancin Honarabul Kehinde Odebunmi a jihar Ekiti.

‘Yan tawaren su na ganin cewa a kotun koli ne za ayi masu adalci a rikicinsu da kishiyoyin na su.

Adesua ya nuna cewa ba za su ja da baya ba, ya yi kira ga magoya bayansu da su dage da yi wa jam’iyyar PDP yakin neman zaben gwamna da za ayi a 2022.

Babban kotun da ke zama a garin Ado-Ekiti, ta goyi bayan hukuncin da babban kotun tarayya ta yi.

KU KARANTA: Shugaban CPC na farko da aka yi, ya ce ana shiryawa Bola Tinubu

Rikicin Ekiti: Za mu kai bangaren Ayo Fayose kotun koli inji mutanen Olujimi
Tsohon Gwamnan Ekiti, Ayo Fayose
Source: UGC

Idan za ku tuna Alkali N Orji–Abadua a shari’a mai lamba ta CA /EK / 57 / 2020, ya zartar da cewa kotun tarayya ta yi daidai ta yi fatali da kukan ‘ya ‘yan tawaren.

Mai shari’a N Orji–Abadua ya dogara da cewa sabanin ‘yan tawagar Sanata Olujimi da mutanen tsohon gwamna Ayodele Fayose, rikicin cikin-gida ne na PDP.

Tun a 2019 ku ka ji cewa ana ta rigima tsakanin Sanatar Ekiti da Fayose a kan zaben shugaban kasa. Wannan ya sa aka yi ta kokarin yi masu sulhu ta cikin gida.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel