Ana rigima tsakanin Sanatar Ekiti da Fayose a kan zaben Atiku

Ana rigima tsakanin Sanatar Ekiti da Fayose a kan zaben Atiku

Shugaban marasa rinjaye a majsaliar dattawan Najeriya, Sanata Biodun Olujimi, ta zargi tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose, da yunkurin yin kane-kane a shirin yakin neman zaben Atiku Abubakar.

Ana rigima tsakanin Sanatar Ekiti da Fayose a kan zaben Atiku

Rikicin Sanata Olujunmi da Ayo Fayose ya ki karewa a Ekiti
Source: Depositphotos

Biodun Olujimi ta na kukan cewa Ayo Fayose ya jefa manyan mukarraban sa cikin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP a zaben 2019, don haka babbar Sanatar ta nemi uwar jam’iyyar PDP ta dauki mataki.

Sanata Olujunmi wanda tana cikin manyan PDP a jihar Ekiti da ma kasar Yarbawa tayi kira shugaban PDP na kasa watau Prince Uche Secondus ya ruguza wannan kwamitin yakin neman zabe na Atiku da aka kafa a jihar Ekiti.

Sanatar ta rubuta korafi ne kwanaki bayan ta gana da wasu jagororin PDP a garin Ado Ekiti. An yi wannan zama ne domin ganin yadda za a dinke barakar da ta shigo cikin jam’iyyar tsakanin tsoho gwama Fayose da Sanatar.

KU KATANTA: An samu baraka bayan an Jam’iyyar PDP ya rabu a Ekiti

Sanata Biodun Olujumi ta bayyana cewa an canza ‘yan kwamitin da za su taya Atiku Abubakar yakin neman zabe a PDP. Daga cikin sauye-sauyen da ta ce an yi shi ne an jefa sunayen Dipo Anisulowo da kuma Gboyega Oguntuase.

Haka kuma ‘yar majalisar tace an cusa sunayen Jackson Adebayo a matsayin kakakain kwamitin tare da kuma wani babban hadimin tsohon gwamnan watau Lere Olayinka a matsayin Darektan yada labarai na kwamatin yakin zaben.

A takardar da Sanatar ta rubuta, ta gargadi jam’iyyar PDP cewa idan ba ayi sulhun cikin gida ba, jam’iyyar APC na iya tika PDP da kasa a zaben shugaban kasa da za a kara tsakanin Buhari da Atiku, duk da farin jinin PDP a jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel