Hotunan ganawar Zulum ta farko da sabbin hafsoshin tsaro, ya mika manyan bukatu 3
- Gwamna Zulum na jihar Borno ya gana da sabbin hafsoshin tsaron kasar nan a Maiduguri
- Ya yi kira garesu da su cigaba da matsantawa 'yan ta'adda ta hanyar hana su sakat a kasar nan
- Ya bukaci hadinn kai tsakaninsu da farar hula tare da dakarun sojin kasashe masu maakwabtaka da Najeriya
Sabbin hafsoshin tsaron kasar nan sun kai ziyararsu ta farko jihar Borno, jihar da ta kasance filin daga da 'yan Boko Haram.
Sun samu ganawa da Gwamna Zulum a Maiduguri, tsohon gwamnan jihar, Sanata Kashim Shettima ya samu halartar zaman.
Shugaban ma'aikatan tsaro, manjo Janar Leo Irabor ya jagoranci shugaban sojin tudu, Manjo Janar Ibrahim Attahiru, shugaban sojin ruwa Rear Admiral Awwal Zubairu Gambo da shugaban sojin sama, Air Vice Marshal isiaka Oladayo Amao zuwa gidan gwamnatin jihar.
KU KARANTA: Gagarumar sarƙaƙiya a kan mutuwar mai aikin wata mata a Kano
A yayin jawabi garesu, Gwamna Zulum ya yi kira ga shugabannin tsaron da su hada kai da dakarun kasashen da ake makwabtaka da su da suka hada da Chadi, Kamaru da jamhuriyar Nijar.
Zulum ya bukaci hadin kai tsakanin dakarun sojin da farar hula domin a rufe gibin da zai iya kawo cin amana sannan sojin su samu bayanan sirri domin hakan ne hanyar samun nasara.
Zulum ya yi kira ga sabbin shugabannin tsaro da su karba kalubale da caccaka da za su iya samu daga jama'a.
Gwamna Zulum ya ce domin samun nasarori, dole ne ya kasance akwai tsaro da hadin kai daga dukkan jami'an tsaro.
Ya kara da bukatar dakarun da su cigaba da aikin da suke yi na hana 'yan ta'adda sakat tare da toshe dukkan hanyoyin kaiwa da kawowarsu a yankin.
KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Wani dan majalisa ya rasu bayan fama da rashin lafiya
A wani labari na daban, Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu ya sa hannu bayan amincewa da sabbin dokoki biyar a jihar.
Kamar yadda takardar da Antoni Janar kuma Kwamishinan shari'a ta jihar, Hajiya Rahmatu Adamu Gulma ta gabatar ga manema labarai, tace Model Penal Code 2021 ta tanadar da hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da laifin garkuwa da mutane a jihar Kebbi a karkashin sashi na 247.
Sannan duk wanda aka kama da laifin yin fyade, karkashin sashin doka ta 259 yanki na 1, hukuncin daurin rai da rai ne.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng