Yanzu yanzu: 'Yan PDP sun yi arangama da jami'an tsaro a Ebonyi

Yanzu yanzu: 'Yan PDP sun yi arangama da jami'an tsaro a Ebonyi

- An yi arangama tsakanin yan sanda da wasu mambobin jam'iyyar PDP tsagin Udogu a Ebonyi

- Yan jam'iyyar tsagin Udogu sun tafi za su shiga sakatariyar jam'iyyar da ta dade a rufe ne sai yan sandan suka zo suka tarwatsa su

- Kakakin jam'iyyar tsagin Udogu, ya yi tir da kama shugaban matasa da wasu mambobinsu da yan sandan suka yi

An yi arangama tsakanin wasu mambobin tsagin jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) a Abakaliki babban birnin jihar Ebonyi a sakatariyar jam'iyyar, The Nation ta ruwaito.

Hakan ya biyo bayan yunkurin da tsagin Fred Udogu suka yi ne na mamaye sakatariyar. An dade da rufe sakatariyar tun bayan rabuwar jam'iyyar zuwa tsagi biyu.

Yanzu yanzu: Yan PDP sun yi arangama da jami'an tsaro a Ebonyi
Yanzu yanzu: Yan PDP sun yi arangama da jami'an tsaro a Ebonyi. Hoto: @MobilePunch
Source: UGC

DUBA WANNAN: Dan majalisar APC ya bindige ɗan fashi da makami har lahira a Sokoto

Jam'iyyar ta rabu ne sakamakon komawa jam'iyyar All Progressive Congress (APC) da gwamnan Jihar David Umahi ya yi.

Kwamitin shugabannin jam'iyyar na PDP a watan Nuwamban bara, bayan ficewar jam'iyyar sun rushe kwamitin gudanarwa wacce Onyekachi Nwebonyi ke yi wa jagoranci.

Jam'iyyar kuma ta kafa sabuwar kwamitin shugabannin riko karkashin jagorancin Fred Udogu.

Sai dai Mista Nwebonyi da sauran mambobin kwamitin gudanarwa na jihar sun kallubalanci rushe su inda suka shigar da kara babban kotun jihar.

Bayan matsaloli da aka samu a karar, Fred Udogu ya sake shigar da kara a babban kotun Abuja.

Tsagin sun kuma samu izini daga kotu na haramtawa kwamitin Nwebonyi gabatar da kansu a matsayin shugabannin jam'iyyar.

KU KARANTA: Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da yasa aka ga Buhari ba takunkumi a fuskarsa a Daura

Sakamakon wannan umurnin na kotu, tsagin Udogu sun yi yunkurin zuwa su shiga sakatariyar a ranar Litinin.

Daruruwar mambobin jam'iyyar tsagin na Udogu sun mamaye sakatariyar jam'iyyar misalin karfe 10 na safe amma jami'an tsaro suka zo suka tarwatsa su.

Jami'an tsaron sun kama wasu daga cikin mambobin ciki har da shugaban matasa na tsagin Udogu, Obinna Iteshi.

Sakataren watsa labarai na tsagin Udogu, Silas Onu ya koka kan kama shugaban matasan da wasu mambobin jam'iyyar.

Ya ce, "A yau, munyi bakin cikin ganin wadanda aka dora wa alhakin kare alummar Ebonyi ne ba su muntunta su."

Da aka tuntube shi, kakakin yan sandan jihar, Aliyu Garba ya ce yana kokarin yin sulhu ne a kan lamarin.

"Ku sake kira na anjima, yanzu na ke kokarin yin sulhu kan batun," in ji shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel