Buhari ya tashi daga baccinsa, ya yaki 'yan bindiga dake 'bayan gidansa', Obasanjo

Buhari ya tashi daga baccinsa, ya yaki 'yan bindiga dake 'bayan gidansa', Obasanjo

- Olusegun Obasanjo, tsohon shugaban kasan Najeriya ya yi kira ga Buhari a kan hauhawar ayyukan 'yan bindiga

- Ya bukaci shugaba Buhari da ya gaggauta shawo kan matsalar tsaron kasar nan domin ya samu suna nagari

- Obasanjo ya ce akwai yuwuwar shugaba Buhari bai taba fuskantar irin wannan kalubalen bane shiyasa ya kasa magance shi

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce abun damuwa ne yadda 'yan bindiga ke cin karensu babu babbaka a yankin arewa maso yammacin kasar nan inda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito daga.

Obasanjo ya bukaci shugaban kasa da ya tashi daga baccinsa kuma ya yaki 'yan bindiga da sauran masu laifuka ballantana a yankin arewacin kasar nan, Punch ta ruwaito.

Tsohon shugaban kasan wanda yayi magana a wata tattaunawar yanar gizo a ranar Lahadi tare da Toyin Falola, ya ce Buhari ya fara tunanin yadda zai bar tarihi mai kyau.

KU KARANTA: Gagarumar sarƙaƙiya a kan mutuwar mai aikin wata mata a Kano

Buhari ya tashi daga baccinsa, ya yaki 'yan bindiga dake 'bayan gidansa', Obasanjo
Buhari ya tashi daga baccinsa, ya yaki 'yan bindiga dake 'bayan gidansa', Obasanjo. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

Ya ce, "A tunanina na san Shugaban kasa Buhari saboda yayi aiki tare da ni. Amma na kan tambaya mutane ko dai ban san Buhari bane ko kuma ya sauya daga yadda na san shi ne? Ba wai na yadda da cewa an sauya mana wani Buhari bane daga Sudan da sauran rashin hankali.

"Daga abinda yayi a kasar nan yayin da yake shugaban kasa, a tunanina zai yi kokari wurin yaki da rashawa. Ta yuwu saboda bai saba fuskantar irin wannan matsalar bane yayin da yayi aiki da ni."

Tsohon shugaban kasan ya kara da cewa wasu gwamnonin a halin yanzu basu da alkibla saboda shugaban kasan bai san yadda zai shawo kan matsalar tsaro a kasar nan ba.

A cikin kwanakin nan, kalubalen tsaron kasar nan sun dauka wata hanya, lamarin da kowa yake kuka da shi.

KU KARANTA: Bata-gari sun kai wa kwamishina hari, sun hargitsa wurin rijistar jam'iyyar APC

A wani labari na daban, kasa da sa'o'i 24 bayan fara aikin sabon shugaban hafsin sojin kasa, Manjo Janar Ibrahim Attahiru, mayakan ta'addanci na Boko Haram sun kai hari garin Dikwa da ke karamar hukumar Dikwa ta jihar Borno.

Bayan maye gurbin shugabannin tsaro na kasar nan a ranar Talata, shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya yi bidiyo cike da takama inda yace sabbin hafsoshin tsaron ba za su iya yin komai a kansu ba.

An gano cewa mayakan ta'addancin masu tarin yawa sun tsinkayi garin Dikwa a motocin yaki inda suka yi musayar wuta da dakarun soji yayin da mazauna garin suka dinga tserewa daji.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng