Hukumar kula da tashoshin jirgin sama ta yi Alla-wadai da tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari
Hukumar kula da tashoshin jirgin sama ta yi Alla-wadai da tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alh. Abdulaziz Yari, bisa abinda yayi ya saba ka'ida a tashar jirgin Malam Aminu Kano.
Bayan saba doka, Hukumar ta ce Yari ya ci mutuncin ma'aikacin muhalli ta hanyar bangajeshi.
Ya aikata hakan ne ranar asabar, 11 ga watan yuli, 2020.
A takardar da hukumar ta saki a shafinta na Tuwita, ta ce AbdulAziz Yari ya ki amincewa a tsaftace jakunkunansa da yake niyyar shiga jirgi da su.
Jawabin yace: "Hukumar kula da jiragen sama a Najeriya (FAAN) ta yi Alla-wadai da dabi'ar tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alh AbdulAziz Yari, wanda ya take dokokin kiwon lafiya yayinda yayi niyyar tafiya ta tashar jirgin saman Malam Aminu Kano a ranar asabar."
"Ya ki bin dokokin da gwamnatin tarayya ta gindaya ta kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da cutar COVID19, PTF, ta hanyar bangaje jami'in kyautata muhallin da ya bukaci tsaftace jakansa. Tsohon gwamnan yana ikirarin cewa shin ba'a san shi mai alfarma bane?"
"Wannan irin rashin da'an na iya sanya rayukan fasinjoji cikin hadari kuma ba zamu amince da hakan ba."
"Saboda haka FAAN tana kira ga fasinjoji, musamman masu alfarma, su taimaka su bi umurnin fadar shugaban kasa wajen bin dokokin da aka gindaya domin kare rayukan kowa daga cutar Coronavirus."
KU KARANTA: Matukiyar jirgin yakin Najeriya mace ta farko ta rasu
A bangare guda, Shugaban kamfanin jirgin saman Aero Contractors, Ado Sanusi, ya shawarci fasinjojin dake fama da mura ko zazzabi kada su zo tashar jirgin sama saboda gudun abinda ka iya biyo baya idan sukayi atishawa.
Yayinda yake jawabi a shirin Sunrise Daily na tashar Channels TV, ranar Alhamis, Sanusi yace za'a killace duk wanda yayi atishawa cikin jirgin saboda za'a daukeshi mai cutar Korona.
Yace: "Ina son bayyanawa mutane cewa idan kanada ciwon zazzabin sauro ko mura, kada ka zo tashar jirgin sama saboda akwai yiwuwan a hanaka shiga cikin jirgi."
"Wannan shine sabon halin da muka samu kanmu."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: `https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng