Gagarumar sarƙaƙiya a kan mutuwar mai aikin wata mata a Kano

Gagarumar sarƙaƙiya a kan mutuwar mai aikin wata mata a Kano

- An cigaba da saka da warwara a jihar Kano bayan mutuwar wata 'yar aiki mai shekaru 16 bisa dalilin mutuwarta

- Duk da dai wata wacce suke aiki tare ta sanar da yadda wacce suke yi wa aiki tayi mata duka har ta kai ga ta kasa tashi ta mutu

- Duk da dai wasu sun ce cizon mage ne yayi sanadiyyar mutuwar yarinyar, don wacce take yi wa aiki ta ce daga baya ta san ta mutu

An cigaba saka da warwara bayan mutuwar wata mai aiki 'yar shekara 16 a Kano, inda mutane da dama suka yi ta bayar da bayanai akan mutuwar ta.

Wacce suke aiki tare ta sanar da Daily Trust cewa wacce suke yi wa aiki ce tayi ta dukanta har sai da ta mutu.

'Yan sanda kuma sun sanar da yadda suka samu labarin cewa cizon mage ne yayi sanadiyyar mutuwarta, kamar yadda matar da ake zargi ta sanar.

Al'amarin ya faru ne a Sharada Salanta wuraren tsakiyar Kano a ranar bayan matar ta koma gida ta ga yarinyar, Khadija Rabi'u, bata yi ayyukanta ba.

KU KARANTA: Boko Haram sun kai hari Dikwa, sun ce sabbin hafsin soji basu isa su hana su komai ba

Gagarumar sarƙaƙiya a kan mutuwar mai aikin wata mata a Kano
Gagarumar sarƙaƙiya a kan mutuwar mai aikin wata mata a Kano. Hoto daga @daily_trust
Source: Twitter

An rufe gidan da lamarin ya faru a ranar Alhamis. Yanzu haka matar da ake zargin ta daki Khadija har ta yayi sanadiyyar mutuwarta ta barbada mata yaji a al'aurarta tana hannun 'yan sanda.

Wata ganau, Rafi'a Muhammad, wacce itama 'yar aikin matar ce ta sanar da Daily Trust cewa matar ta bukaci ta taya ta dukan marigayiya Khadija.

Rafi'a tace sun koma gidan tare da Khadija inda wacce suke yi wa aiki ta tambayeta dalilin da ya sanya bata yi ayyukanta ba, inda tace bata da lafiya. Take anan ta fara ta dukanta har ta gayyatar ta don ta taya ta.

Ta fara taya ta dukan bayan matar ta gama zaginta, sai ta lura numfashinta ya fara daukewa.

Matar ta cigaba da dukanta har da sanya mata wani karfe a al'aurarta, daga nan ta bada mata yaji a al'aurar. Bayan ganin numfashinta ya dauke ne ta kai ta asibiti su kuma suka ki amsarta sai ta kawo dan sanda.

Malama Ummalkhairi Shehu da tayi wa gawar Khadija wanka ta bayyana yadda duk jikinta yayi kaca-kaca da ciwuka.

Amma kakakin 'yan sanda, DSP Haruna Abdullahi Kiyawa ya ce ana zargin cizon magen da yayi sanadiyyar mutuwarta

KU KARANTA: Jerin sunaye: Shugabannin dakarun sojin kasa na Najeriya tun daga 1999 da jihohinsu

A wani labari na daban, tsohon hafsin sojan kasa, Laftanal Janar Tukur Buratai mai murabus, ya ce ya gyara harkar sojin Najeriya fiye da yadda ya sameta.

Ya furta hakan ne a wani taron faretin saukarsa daga kujerarsa a ranar Juma'a a Abuja, Daily Trust ta wallafa. Ya kara da cewa ya tabbatar da cewa ya bai wa sojojin cikakkiyar horarwa da kuma inganta walwalarsu.

Kamar yadda yace "Yau ranar farinciki ce ba ta takaici ba, saboda zan yi murnar barin sojojin Najeriya fiye da yadda na same su.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel