A rufe fuske da tsumma domin gujewa dokar zaman gida inji Fadar Shugaban kasa

A rufe fuske da tsumma domin gujewa dokar zaman gida inji Fadar Shugaban kasa

- Fadar Shugaban kasa ta yi kira a rika bin dokar rufe fuska da bada tazara

- Shugaba Muhammadu Buhari ya samu rahoto cewa ba a bin wannan doka

- Buhari ya ja-kunnen al’umma su guji yin abin da zai kai ga dawo da kulle

Fadar shugaban kasar Najeriya ta yi kira ga babbar murya ga al’umma su bi doka da sharudan yaki da cutar COVID-19, ta hanyar rufe fuskokinsu.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci jama’a su rika rufe fuska kamar yadda ya bada umarni, domin su guji halin da zai kai a sake kakaba dokar kulle.

Jawabin shugaban kasar ya fito ne daga bakin mai magana da yawunsa, Garba Shehu a ranar Lahadi.

Da yake magana ta shafinsa na Twitter, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa fadar shugaban kasa ta ji mutane na watsi da dokar bada tazara da rufe fuska.

KU KARANTA: Buhari ya maida martani ga masu sukar Gwamnatinsa

“Fadar shugaban kasa ta damu da rahoton rashin bin sabuwar dokar da shugaban kasa ya sa wa hannu wanda ta wajabta rufe fuska da bada tazara a bainar jama’a.”

Jawabin ya ce: “Ana kira ga ‘yan Najeriya su bada hadin-kai sosai wajen nasarar wannan tsari.”

“Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kawo wannan dokar ne da kyakkyawar zuciya, ba da nufin ya yi wa wasu jama’a ukuba ba.” Inji Hadimin shugaban kasar.

Shehu ya kara da cewa: “Fadar shugaban kasa ta na roko ga gwamnatocin jihohi, sarakuna da malamai su wayar da kan jama’a da tabbatar da an bi wannan doka.”

KU KARANTA: Shugaban kasa ya zabi sabon Dogari

A rufe fuske da tsumma domin gujewa dokar zaman gida inji Fadar Shugaban kasa
Shugaban kasa da takunkumi Hoto: @NgrPresident
Asali: Twitter

A cewarsa, gwamnatin Buhari ta na gudun a garkame gari saboda tasirin hakan ga tattalin arziki, ya ce hanyar da za a guje wa hakan, shi ne a bi matakan da aka kawo.

Buhari ya ce nauyi ya rataya a kan kowa ya kare kansa, tun da babu mai rigakafin wannan cuta.

A baya kun ji cewa wasu gwamnonin jihohi 7 a yankin Arewacin Najeriya za su mori tallafin makudan kudi har fam $900,000 domin rage radadin annobar COVID-19.

Asusun rallafawa noma na kasa da kasa, IFAD, ya ba da tallafi na farko na dala $900,000 da nufin tallafa wa ƙananan 'yan kasuwa da wadanda ke karkara a yankin Arewa.

Rahoton ya ce za a bada kudin ne ga wadannan Bayin Allah da annobar COVID-19 ta rutsa da su.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel