Matasan arewa sun bukaci sabbin hafsoshin Najeriya su kasance masu amana
- Wata kungiyar matasa ta arewacin Najeriya ta bukaci sabbin hafsoshin da Buhari ya nada su zama masu amana
- Sun bayyana cewa nadasu da aka yi an yi shine bisa duba cancanta da jajircewa kan aiki
- Sun kuma nuna godiyarsu ga shugaba Buhari kan karbar shawarin al'umma wajen gudanar da sauyin
Wata kungiya, Arewa Youth Initiative for Peace and Good Leadership, ta yi kira ga sabbin shugabannin rundunonin da aka nada da su nuna kishin kasa da cikakkiyar gaskiya wajen gudanar da ayyukansu, The Nation ta ruwaito.
Matasan, wadanda suka yi magana ta bakin Shugabansu, Mohammed Rilwanu, a cikin wata sanarwa, sun yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari saboda sauraren muryar mutane ta hanyar sallamar tsoffin shugabannin rundunonin.
Sun shawarci sabbin wadanda aka nada su fito da sabbin dabarun fada.
KU KARANTA: EFCC ta damke wasu daliban makarantar damfara a Abuja
A cewarsu: ‘’Yakamata sabbin shugabannin rundunonin su guji ayyukan bata gari yayin gudanar da ayyukansu; rashawa tana haifar da mummunan shugabanci wanda ka iya haifar da gazawa.
’’Bai kamata su ga wannan nadin a matsayin wata dama ta wawure kudade ba, wata dama ce a gare su su bar kyawawan suna mai dorewa wanda ‘yan Najeriya ba za su manta da shi ba.
‘’Wannan nadin wata dama ce a gare su don baje kolin hikimarsu da amintuwa da kare ‘yan Nijeriya da dukiyoyinsu kamar yadda ya bayyana karara a Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya.”
Kungiyar ta kuma bukaci Shugaban kasar da ya mutunta tanade-tanaden kundin tsarin mulki da kuma ka'idar talayyar tarayyar Najeriya.
ya ce: “Duk nade-naden gwamnatin tarayya ya kamata ya zama ta hanyar cancanta kuma halayyar tarayya ya kamata a kiyaye ko yaushe kamar yadda yake a bayyane a cikin kundin tsarin mulki saboda Najeriya ta kasance ta dukkan 'yan kasa ’’.
‘’Ci gaba da rashin kulawa da wata kabila ta asali a nadin shugabannin aiyuka lallai hakan na haifar da damuwa."
KU KARANTA: An ceto wasu daga matasan takum 25 da aka sace
A wani labarin, Sojojin Najeriya tare da goyon bayan kungiyar hadin gwiwa ta Multinational Joint Taskforce, MNJTF, sun mamaye wasu yankuna hudu na Boko Haram a Arewa maso Gabas.
An bayyana nasarar ne 'yan sa'o'i bayan sanarwar sabbin hafsoshin soja. Aikin da Brig. Gen Waidi Shaibu, Birgediya kwamandan runduna ta musamman ta 21, ya afkawa mayakan Boko Haram da dama a Maiyanki, Darulsallam, Bula Kurege da Izza.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng